Nasarori da cece-ku-ce da abubuwan mamaki sun dabaibaye zaɓukan fid da gwanin ‘yan takarar Majalisar Wakilai na jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, wanda aka gudanar a jihohin ƙasar gabanin zaɓukan gama gari na shekarar 2027.
Zaɓukan fid da gwanin, waɗanda tun farko aka shirya gudanarwa ranar Juma’a amma daga baya aka ɗaga su zuwa Asabar, sun samar da ‘yan takarar da aka cimma matsaya a kansu ta hanyar sulhu, tare da nasarori masu cike da cece-ku-ce sakamakon tashin hankali, zargin ƙaƙaba ‘yan takara da kuma wasu korafe-korafe da suka biyo baya.
Yayin da aka samu waɗanda suka yi nasara a mafi yawan mazaɓu, zaɓukan sun fuskanci rashin jituwa a jihohi irin su Ondo da Ekiti da Katsina da Neja.
Tsarin sauraron ƙorafe-ƙorafe a Ondo
A jihar Ondo, jam’iyyar APC ta gayyaci masu neman takara da ba su gamsu da sakamakon zaɓen ba da su miƙa ƙorafe-ƙorafensu ga kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafen jam’iyyar.
A wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jihar, Alex Kalejaye, ya fitar ranar Asabar, ya ce kwamitin zai zauna a sakatariyar jam’iyyar da ke kan titin Olu Obasanjo a Akure domin sauraron koke-koken masu neman tikitin takarar Majalisar Wakilai.
“Jam’iyyar ta yi kira ga masu neman takara su yi amfani da damar da kwamitin ya bayar domin gabatar da ƙorafe-ƙorafensu cikin adalci,” in ji sanarwar.
Kalejaye ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da zama har sai an warware dukkan ƙorafe-ƙorafen domin tabbatar da haɗin kai da adalci a cikin jam’iyyar.
An ayyana zaɓen Ekiti a matsayin wanda bai kammala ba
A jihar Ekiti kuwa, jam’iyyar APC ta ayyana zaɓen fid da gwani na mazaɓar tarayya ta Oye/Ikole a matsayin wanda bai kammala ba bayan tashin hankali a wuraren zaɓe.
Shugaban kwamitin zaɓen fid da gwanin Majalisar Wakilai, Asipa Wasiu, ya ce ba a kammala tsarin zaɓen ba sakamakon wasu rikice-rikice, inda ya ce kwamitin aiki na ƙasa na jam’iyyar ne zai yanke hukuncin mataki na gaba.
“Kamar yadda kowa ya sani, muna da mazaɓun tarayya shida a Ekiti. Amma batun Ekiti ta Arewa, wanda ya haɗa da Oye da Ikole, yanzu yana hannun kwamitin aiki na ƙasa,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki su jira ƙarin umarni daga uwar jam’iyyar.
Duk da haka, an samu waɗanda suka yi nasara a sauran mazaɓu biyar.
Ɗanmajalisar mai ci Steve Olusola Fatoba ya samu tikitin takara a mazaɓar Ekiti ta Tsakiya ta I da ƙuri’u 8,943.
Oladapo Karounwi ya kayar da ɗanmajalisar mai ci Abiodun Omoleye a Ekiti ta Tsakiya ta II, inda ya samu ƙuri’u 6,573 kan 2,096.
A Ekiti ta Kudu ta I kuwa, Okoro Toyin Zaccheaus ya yi nasara da ƙuri’u 9,798, yayin da ɗanmajalisar mai ci Rufus Adeni Ojuawo ya samu ƙuri’u 1,842.
Ɗanmajalisar mai ci Richard Bamisile ya sake samun tikitin takarar Ekiti ta Kudu ta II da ƙuri’u 4,379, yayin da Ibrahim Olanrewaju ya kayar da Kolawole Akinlayo a Ekiti ta Arewa ta II da ƙuri’u 6,856 kan 2,102.
Abokan Wike sun mamaye zaɓen Ribas
A jihar Ribas, wasu ‘yan siyasa masu alaƙa da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, sun samu tikitin takarar APC.
Daga ciki har da shugaban Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martins Amaewhule, wanda ya samu tikitin mazaɓar Obio/Akpor da ƙuri’u 17,968.
Ɗanmajalisar mai ci Dumnamene Dekor ya riƙe tikitin mazaɓar Gokana/Khana bayan da ya doke Israel Ngbuelo da ƙuri’u 17,073 kan 1,220.
Sauran waɗanda suka yi nasara sun haɗa da Solomon Bob da Frederick Apiafi da Igwe Precious da Blessing Amadi da Cyril Hart da Isobo Jack da Felix Nwaeke da Victor Obuzor da Chibuzor Nwamaka da Nyebuchi Joy da Linda Stewart.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen a Port Harcourt, shugaban kwamitin zaɓen, Wahab Owokoniran, ya ce an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
“Ina sanar da duniya cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana. Ba mu samu tashin hankali ko wata matsala ba,” in ji shi.
Abin mamaki a Filato
A jihar Filato kuwa, da fari an samu rahaotannin da ke cewa ɗanmajalisar mai ci Yusuf Gagdi ya kasa samun tikitin takara domin sake neman wa’adi.
Rahotannin farkon sun ce Gagdi, wanda ke wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanke/Kanam, ya sha kaye a hannun John Tonshinen a zaɓen fid da gwanin.
Tonshinen ya samu ƙuri’u 299,968, yayin da Gagdi ya samu ƙuri’u 5,849, sannan wani ɗan takara Hopar Gopbia ya samu ƙuri’u biyar.
Amma daga bisani sai aka ga matar Gagdi, kuma fitacciyar mai amfani da shafukan sada zumunta, Lailah Ali Othman ta wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda jami’in APC na jihar yana ayyana Gagdi a matsayin wanda ya yi nasara.
An gudanar da zaɓe cikin lumana a Ebonyi
A jihar Ebonyi, Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana zaɓukan fid da gwanin a matsayin waɗanda aka gudanar cikin lumana da tsari.
Da yake magana kan masu korafi da suka fice daga jam’iyyar saboda buƙatun siyasarsu, gwamnan ya ce hakan ya dace da tsarin dimokraɗiyya.
“Waɗanda suke korafi suna yin hakan ne bisa tsarin dimokraɗiyya,” in ji shi. “Abin farin ciki shi ne zaɓen ya gudana cikin lumana kamar yadda aka tsara.”
Daga cikin waɗanda suka yi nasara akwai Chinedu Ogah daga Ikwo/Ezza ta Kudu da Iduma Igariwey daga Afikpo/Edda da kuma Nkemkanma Kama daga Ohanivo.
Zargin tsare ɗan takara a Katsina
A jihar Katsina, wani tsohon mai neman takara a mazaɓar Mani/Bindawa, Ahmed Saleh, ya yi zargin cewa jami’an tsaro sun tsare shi sama da sa’o’i 24 domin hana shi shiga zaɓen fid da gwani.
Saleh ya ce an tsare shi ne bisa umarnin gwamna Dikko Umaru Radda.
Duk da rashin kasancewarsa wajen zaɓen, ya samu ƙuri’u 1,256, yayin da Jamila Mani, mai bai wa gwamnan shawara kan ilimin yara mata da ci gaban yara, ta yi nasara da ƙuri’u 24,989.
Sauran sakamakon a faɗin ƙasar
A jihar Katsina, Yusuf Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya samu tikitin takara a mazaɓar Daura.
A Kaduna, shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Tajudeen Abbas, ya samu tikitin takara a mazaɓar Zaria ba tare da hamayya ba.
Tsohon ɗanmajalisa Samaila Suleiman ya samu tikitin Kaduna ta Arewa, yayin da sauran ‘yan takara suka fito daga sassa daban-daban na jihar.
A jihar Kebbi kuwa, tsohon babban kwanturolan gidan gyaran hali na Nijeriya, Jafar Ahmed Jega, ya kayar da ɗanmajalisar mai ci Mansur Musa Jega wajen samun tikitin mazaɓar Jega/Gwandu/Aleiro.
Tsohon ministan jinƙai, Yusuf Tanko Sununu, ya fito a matsayin ɗan takarar APC a mazaɓar Yauri/Shanga/Ngaski.
Zanga-zanga a Neja da Kebbi
A jihar Neja, wasu mazaɓu sun fuskanci zanga-zanga sakamakon zargin ƙaƙaba ‘yan takara.
Rahotanni sun ce zaɓukan fid da gwani na mazaɓar Gurara/Tafa/Suleja da Shiroro sun tsaya cik saboda rashin jituwa tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Haka kuma a Kebbi, magoya bayan Bashar Suleman Bajida sun gudanar da zanga-zanga bayan fitowar ɗanmajalisa mai ci Kabir Ibrahim Tukura a matsayin wanda ya samu tikitin mazaɓar Zuru/Fakai/Sakaba/Danko Wasagu, suna zargin wasu shugabannin jam’iyyar da yin katsalandan a tsarin zaɓen.
Zaɓukan fid da gwanin dai wani ɓangare ne na shirye-shiryen APC domin zaɓukan gama gari na shekarar 2027, yayin da ake sa ran gudanar da zaɓukan fid da gwani na majalisar dattawa da sauran muƙamai a kwanaki masu zuwa.












