| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta ƙayyade kuɗin gidajen haya
Sabon shirin ƙayyade kuɗin hayan Nijar zai ƙayyade iya kuɗin da za a iya karɓa a matsayin kuɗin haya bisa unguwannin tare da tanadin zaman kaso ga waɗanda suka saɓa wa dokar.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta ƙayyade kuɗin gidajen haya
Janar Tiani / Reuters

Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani, ya rattaba hannu kan wata doka da za ta ƙayyade kuɗin haya na gidajen zama a fadin Nijar, inda kuɗaɗen za su dangana ga unguwanni da irin yanayin gidajen.

Dokar wadda aka wallafa ranar 22 ga watan Afrilun shekarar 2026, ta ƙayyade kuɗaɗen haya kan gidaje da ke rukunun F2 wato mai daki biyu da F3 mai ɗaki, yayin da ya ware gidajen da ke rukunin F4 ai ɗaki huɗu da F5 mai ɗaki biyar.

A gidajen haya , kuɗaɗen haya na gidajen da ke rukuni na F2 an ƙayyade su ne tsakanin kudin sefa 20,000 zuwa 40,000 (kimanin dala $34 to $68) bisa tsayuwarsa, yayin da kudin hayan waɗanda ke rukunin F3 zai kama ne daga sefa 45,000 da sefa 80,000 (kimanin dala $76 zuwa $136).

A wasu wuraren kuma, iya kuɗin da aka ba da damar karɓa sun kama ne daga sefa 15,000 zuwa sefa 60,000 (kusan dala $25 zuwa dala $102).

Dokar ta kuma ƙayyade cewa duk wani ƙarin kuɗin haya kada ya wuce kashi 10 cikin 100 a kan kudin da ake biya kuma ƙarin zai faru ne kawai idan aka samu gyara da zai inganta rayuwar mazauna gidan .

Kazalika dokar ta kuma tanadi uƙuba ta aikata lafuka kan masu gidajen da ba su yi biyayya ga tanade-tanaden sabuwar dokar ba .

Duk wata ƙarya game da sifar gida ko kuma gaza miƙa bayanan hayar ga ƙaramar hukuma cikin watanni uku da ba da hayar ba zai sa mai gidan ya fuskanci uƙuba ta zaman kaso daga kwanaki biyar zuwa kwanaki goma sha biyar, tare da tara ta sefa 50,000 zuwa sefa 99,000 (kimanin dala 85 zuwa dala 168).

Uƙubar za ta iya kai zaman kaso na kwanaki talatin ga masu gidajen da suka karɓi abin da ya ɗara kuɗin da aka ƙayyade wa irin gidajensu, ciki har da karɓar kuɗin ta hanyar da ake ganin ta damfara ce.

Masu karɓar haya kuwa da suka amince da gangan su biya kuɗin hayar da ya saɓa wa dokar da waɗanda suka haɗa baki da su za su faɗa a cikin waɗanda dokar za ta yi aiki a kan su.