A cewar Hukumar Sadarwa ta Turkiyya, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin Firaministan Sudan, Kamil Idris, wanda ke ziyarar aiki a Turkiyya, a Fadar Shugaban Kasa a Ankara.
Hukumar ta bayyana cewa taron na ranar Laraba ya tattauna dangantaka diflomasiyya tsakanin Turkiyya da Sudan, da kuma batutuwan yankin da na duniya, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta wallafa a dandalin sada zumunta na Turkiyya NSosyal.
Erdogan ya ce ƙasashen biyu na nufin ƙara bunƙasa dangantaka ta hanyar matakan da ake da su yanzu da waɗanda za a ɗauka nan gaba, yana mai jaddada cewa Turkiyya na ci gaba da goyon bayan cikakken 'yancin kai da iko kan iyakar ƙasar Sudan.
Shugaban Turkiyya ya ƙara da cewa Ankara na aiki don taimakawa a kawo karshen rikicin Sudan da dawo da zaman lafiya, tare da cewa Turkiyya na tallafawa ƙoƙarin diflomasiyya don tsagaita wuta da ƙaddamar da cikakken tsarin zaman lafiya.
Erdogan ya bayyana cewa tallafin jin ƙai da ake bayarwa da nufin don saukaka wahalar al'ummar Sudan zai ci gaba da ƙaruwa a wannan lokaci.
Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa na Turkiyya Cevdet Yilmaz, da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan, da Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa Alparslan Bayraktar, da Ministan Noma da Raya Gandun Daji Ibrahim Yumakli, da Daraktan Sadarwa Burhanettin Duran.


















