| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An kashe shugabannin Daesh 175 a arewa maso gabashin Nijeriya a farmakin haɗaka da Amurka
Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na hedikwatar tsaron Nijeriya Manjo Janar Samaila Uba ya fitar a ranar Talata ta ce, “Zuwa ranar 19 ga Mayun 2026, binciken farko ya tabbatar da cewa an kawar da ‘yanta’addan Daesh akalla 175 daga fage daga.
An kashe shugabannin Daesh 175 a arewa maso gabashin Nijeriya a farmakin haɗaka da Amurka
Sanarwar ta ce an kashe manyan kusoshin kungiyar da ke da tasiri a duniya da yankin Tafkin Chadi. / Reuters

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta sanar da hallaka shugabannin Daesh aƙalla 175, sakamakon jerin hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’adda tare da Rundunar Hadin Gwiwa ta Amurka a Afirka (AFRICOM) a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Wata sanarwa da hedikwatar ta fitar a ranar Talata ɗauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai Manjo Janar Samaila Uba ta ce, “Zuwa ranar 19 ga watan Mayun, 2026, binciken farko ya tabbatar da cewa an kawar da ‘yanta’addan ISIS aƙalla 175 daga fage daga.”

Baya ga kisan mayakan, hare-haren sun kuma yi sanadiyyar lalata muhimman kayayyaki na kungiyar.

Sanarwar ta bayyana cewa an kawar da shingen bincike na Daesh, da rumbun makamai,  da sansanonin samar da kayan aiki, da kayayyakkin yaki, da kuma hanyoyin hada-hadar kudi da kungiyar ke amfani da su wajen gudanar da ayyukanta na ta'addanci.

Kashe manyan shugabannin ta’addanci

A bangaren kisan shugabannin na Daesh, sanarwar ta ce an kashe manyan kusoshin kungiyar da ke da tasiri a duniya da yankin Tafkin Chadi.

Cikin wadanda aka kashe baya ga Abu-Bilal al-Minuki daya daga cikin manyan jami'an ISIS mafi hadari a duniya a cewar Janar Janar Samaila Uba, akwai kuma Abd-al Wahhab, Babban jagoran kungiyar ISWAP dake da alhakin tsara hare-hare da farfaganda, da Abu Musa al-Mangawi, wani babban jagora a kungiyar Daesh, da Abu al-Muthanna al-Muhajir, babban jami’in watsa labarai na ISWAP kuma na hannun daman Abu-Bilal al-Minuki.

Hedikwatar tsaron ta Nijeriya ta jaddada cewa wannan samame na hadin gwiwa ya kara nuna irin jajircewar da dakarun kasar suka saba nunawa tsawon shekaru wajen farauta da kuma murkushe ‘yan ta’adda a duk inda suke a fadin Nijeriya.

Hukumomin tsaron sun tabbatar wa 'yan ƙasa cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, sannan za a c gaba da hadin gwiwar da har sai an kakkabe duk wani da ke barazana ga tsaron ƙasa da zaman lafiyar yankin baki ɗaya.