| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Amurka za ta kawo ƙarshen yaƙi da Iran 'cikin gaggawa', a cewar Trump
Shugaban Amurka ya ce ya yi amannar cewa za a kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa kuma Tehran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, inda ya ƙara da cewa yana fatan za a warware batutuwan cikin ruwan sanyi.
Amurka za ta kawo ƙarshen yaƙi da Iran 'cikin gaggawa', a cewar Trump
Shugaba Trump ya ce Amurka za ta kawo karshen yakin Iran cikin kankanin lokaci. / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka na ɗaukan matakai cikin sauri wajen kawo ƙarshen yaki da Iran.

"Za mu kawo ƙarshen wannan yaƙi cikin gaggawa. Suna matukar son yin yarjejeniya, sun gaji da wannan yaƙi," kamar yadda Trump ya faɗa a Fadar White House.

"Ina tunanin za mu gama da wannan cikin gaggawa, kuma ba za su sami makamin nukiliya ba, kuma ina fatan za mu kammala shi cikin yanayi mai kyau," kamar yadda ya kara bayyanawa.

Shugaban ƙasa ya kuma jaddada ƙarfin soja na Amurka, yana mai danganta hakan da ayyukan kwanan nan da suka rage ƙarfin Iran.

“Sojojinnmu shi ne mafiya karfi a duniya… Mun kawar da sojojin ruwansu. Sojojinsu na ƙasa sun tafi. Makamansu na harbo jiragen sama sun tafi. Dukkan kayan yaƙin da suke amfani da su don yaƙi ba bu su... Ba na son na ce shugabanninsu sun tafi, saboda ba abu ne mai kyau ba, amma hakan gaskiya ne,” in ji shi.

Trump ya jaddada cewa ba za a bar Iran ta samar da makamin nukiliya a kowane yanayi ba.

"Ba za mu iya barin hakan ta faru ba, kuma ba za mu jure masa ba," in ji shi.

Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da tashin hankali a yankin ya ƙaru tun bayan da Amurka da Isra'ila suka kai hare-hare kan Iran a watan Fabrairu.

Tehran ta mayar da martani da hare-hare kan Isra'ila da kuma ƙawayen Amurka a yanki Tekun Fasha, tare da rufe mashigar Hormuz.

An samu yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu ta hanyar shiga tsakani da Pakistan ta yi, amma tattaunawa a Islamabad ba ta samar da yarjejeniya mai ɗorewa ba. Daga bisani Trump ya tsawaita yarjejeniya ba tare da iyaka ba.

Rumbun Labarai
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take
Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi sake buɗe Hormuz, taƙaita aikin nukiliya: babban jami'i a Iran
An gano wani dutse mai ɗauke da rubutun sunan Khalifa Umar ibn Khattab a Madina
Iran ta kai hare-hare manyan cibiyoyin sojin Amurka 18 a Kuwait da Bahrain yayin da hankula ke tashi
Amurka ta kai hare-hare da dama ta sama Iran yayin da hankula suka tashi kan sake ɓarkewar yaƙi
Helikwaftan sojin Amurka ya faɗi kusa da Mashigar Hormuz; matuƙansa suna 'lafiya', in ji Trump
Ƙungiyar Houthi ta yi barazanar haramta wa Isra'ila jigilar kayayyaki a Bahar Rum gaba ɗaya
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a faɗin Iran yayin da yaƙin Gabas Ta Tsakiya ya sake ɓarkewa
Iraniyawa sun nuna juriya da ƙalubale irin na lokacin yaƙi a wani gagarumin gangami a Tehran
Fashe-fashe sun girgiza tsibirin Qeshm na Iran yayin da Kuwait ta tare jerin makamai masu linzami
Iran ta ce ta kai hari kan wani jirgi mai alaƙa da Amurka da Isra'ila bayan hari kan wani jirginta
Iran ta dakatar da tattaunawa da Amurka saboda hare-haren Isra'ila a Lebanon: rahoto
Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka a Kuwait bayan hari kan benen sadarwar Hormozgan
Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon
Iran ta ci gaba da aikin samar da gas a wurarenta uku na South Pars da ke cikin teku
Netanyahu ya kira taron gaggawa bayan Hezbollah ta kai hari na ban mamaki ga sojin Isra'ila
Zaman jiragen sojojin Amurka ya janyo wa filin jirgin saman Ben Gurion na Israila asarar $248M
Dakarun Juyin-Juya-Hali na Iran sun ce sun kai hari sansanin Amurka na sama a Kuwait
Amurka ta kai sabbin hare-hare a wuraren soji a kudancin Iran — rahoto
Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe shugaban rundunar sojin Hamas a wani babban hari a Gaza