Jamhuriyar Nijar da China sun rattaba hannu kan wasu manyan yarjejeniyoyi a bangaren mai da nufin ƙara yawan haƙo mai tare da rage taƙaddamar da ta dabaibaye alaƙar ƙasashen biyu cikin shekarar da ta gabata.
An sanar da yarjejeniyoyin ne a ranar Litinin yayin wani biki da aka gudanar a Yamai, babban birnin Nijar.
Ana sa ran yarjejeniyoyin za su ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangaren mai tare da bai wa Nijar ƙarin iko kan albarkatun ƙasarta.
Manyan jami’ai daga kasashen biyu sun halarci taron, ciki har da Firaministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine, da Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Bakary Yaou Sangare.
Daga cikin yarjejeniyoyin da aka cim ma har da sake fara wasu manyan ayyukan haƙo mai guda biyu, na Dinga Deep da Abolo-Yogou, wadanda jimillar jarin da za a zuba a cikinsu ya kai kusan dala biliyan daya.
Da yake jawabi yayin bikin, Sangare ya ce ana sa ran ayyukan za su ƙara yawan ɗanyen man da Nijar ke haƙowa daga ganga 110,000 zuwa ganga 145,000 a rana kafin karshen shekarar 2029.
Yarjejeniyoyin sun kuma hada da rage kudin jigilar danyen man Nijar ta bututun mai zuwa kasar Benin.
A cewar jami’ai, an rage kudin jigilar daga dala 27 zuwa dala 15 kan kowace ganga, matakin da ake sa ran zai adana wa Nijar fiye da dala miliyan 106 a shekara.
A wani babban ci gaba kuma, Nijar ta mallaki kaso 45 cikin 100 na kamfanin bututun mai na Afirka ta Yamma, West African Oil Pipeline Company, wani reshe na kamfanin mai na China, CNPC, wanda ke kula da bututun jigilar danyen mai zuwa kasashen waje.
Gwamnatin Nijar ta ce sabbin yarjejeniyoyin za su amfani ma’aikata da kamfanonin cikin gida.
Mahukunta sun ce ana sa ran samar da ayyukan yi kusan 450 ga ‘yan Nijar nan da shekarar 2030, yayin da za a bai wa kamfanonin cikin gida fifiko wajen kwangilolin ayyuka.
Haka kuma jami’ai sun yi alkawarin rage gibin albashi tsakanin ma’aikatan kasashen waje da na cikin gida.
Dangantaka tsakanin Nijar da kamfanonin man kasar China ta yi tsami a watannin baya bayan gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi wasu kamfanoni da karya dokokin ƙwadago na kasar.
A bara, an kori wasu shugabannin kamfanoni da ma’aikatan kasar China masu alaka da CNPC da rassanta daga Nijar.
Rahotanni sun ce tattaunawar warware taƙaddamar ta fara ne a kasar China a watan Yunin 2025, kuma yanzu ta kai ga cim ma sabbin yarjejeniyoyin da ke nuna sabon babi na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Kamfanonin kasar China na aikin haƙo mai a Nijar tun daga shekarar 2011.








