Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Ribas ta sallami wasu jami’anta masu muƙamin sufeto biyar da ke aiki a Sashen Ayyuka na Musamman bisa zargin hannu a fashi da makami, garkuwa da mutane, karɓar kuɗi ta tilas da haɗa baki wajen aikata laifi.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Blessing Agabe, ta fitar a ranar Jumma’a.
Kakakin rundunar ‘yansanda ta ƙasa, Anthony Placid ya ce jami’an sun shiga jerin ayyukan ta’addanci tsakanin watan Satumban 2025 zuwa Janairun 2026 a faɗin jihar Rivers.
Jami’an da aka sallama sun haɗa da John Okoi, Eyibo Asuquo, Udo Ndipmong, Bright Nwachukwu da Anele Ikechukwu.
A cewarsa, an gano lamarin ne bayan wata ƙungiya mai suna Behind Bars Human Rights Foundation ta gabatar da koke-koke a madadin mutane da dama da abin ya shafa.
Ya bayyana cewa jami’an suna amfani da ƙananan motocin haya suna gudanar da bincike ba bisa ƙa’ida ba, inda suke tare mutane da bakin bindiga.
“Jami’an suna tilasta wa waɗanda suka kama su bayyana lambobin sirrin bankinsu da bayanan asusunsu. Daga nan kuma su riƙa tura kuɗi daga asusun bankin mutanen zuwa nasu ta ƙarfin tuwo.
“Haka kuma suna ƙarya suna cewa su jami’an hedikwatar Zone 16 ne da ke Yenagoa domin tsoratar da mutane da kauce wa zargi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa jami’an sun yi kuma garkuwa da wani mutum a kan titin Aba Road inda suka ƙwace Naira miliyan 3.6 da dala 4,000 daga lalitarsa ta kirifto.
Ya ce wani mutum daban kuma an yi garkuwa da shi tare da ƙwace masa fiye da Naira miliyan 7.3 da kayayyaki masu daraja, yayin da wani na uku ya rasa Naira miliyan 1.5 bayan an tare shi a kan titin NTA Road.












