| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Ba mu yanke shawara kan makomarmu ta siyasa ba – Kwankwaso
Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na fuskantar ƙalubale mai girma sakamakon hukuncin Kotun Ƙoli, wanda ya mayar da maganar shugabancin jam’iyyar zuwa Babbar Kotu, don haka ne suke tattaunawa da jam'iyyun NDC da PRP don neman mafita ta siyasa.
Ba mu yanke shawara kan makomarmu ta siyasa ba – Kwankwaso
Kwankwaso ya ce bai ayyana aniyar tsayawa takara ba kuma bai marawa wani dan takara baya ba tukunna.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan siyasar Nijeriya kuma jigo a jam’iyyar ADC Sanata Rab’iu Musa Kwankwaso, ya fitar da wata sanarwa inda fayyace matsayinsa game da ce-ce-ku-cen da ake yi kan makomarsa ta siyasa da kuma matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta.

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafukan sada zumunta da tsakar daren Lahadi, Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na fuskantar ƙalubale mai girma sakamakon hukuncin Kotun Koli wanda ya mayar da maganar shugabancin jam’iyyar zuwa Babbar Kotu.

Ya kuma ambato ƙarin wasu matsalolin inda ya bayyana cewa, “Babbar Kotun Tarayya ta soke babban taron jam’iyyar na baya bayan nan. Sannan Babban Lauyan Gwamnati ya shigar da buƙatar soke rajistar jam’iyyar ADC baki daya a wata Babbar Kotun Tarayya,” in ji Kwankwaso.

Tuntuɓar wasu jam'iyyu

Ya ce kamar yadda suka bar jam’iyyar NNPP sakamakon matsalolin shari’a da aka kunno musu daga waje, yanzu jam'iyyar ADC ma ta tsinci kanta a cikin irin wannan yanayi na rashin tabbas.

Sakamakon waɗannan matsaloli, Kwankwaso ya bayyana cewa kamar yadda sauran masu ruwa da tsaki suke yi, shi ma ya fara gudanar da faffaɗar tuntuɓa gami da tattaunawa da shugabannin jam’iyyun NDC da PRP da sauran jam’iyyu domin lalubo hanyar da za ta kare muradunsu na dimokuraɗiyya.

"Za mu sanar da matsayar mu ta ƙarshe nan ba da jimawa ba bayan mun kammala shawara," in ji Kwankwaso.

Takarar shugaban ƙasa

Game da raɗe-raɗin cewa yana neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa maganganu ba su da tushe. Ya yi karatun baya, inda ya ambato tarihinsa na siyasa a matsayin mai kishin ƙasa da biyayya ga jam'iyya.

Tsohon gwamnan na Kano kuma tsohon sanata ya bayyana cewa har yanzu jam’iyyar ADC ba ta fitar da tsarin raba muƙamai zuwa shiyyoyi ko matsayar takara ba, don haka bai ayyana aniyar tsayawa takara ba kuma bai marawa wani dan takara baya ba tukunna.

Ya bayyana cewa rashin halartar wasu tarukan jam’iyyar ADC da aka yi kwanan nan ya faru ne saboda wasu uzurori na ƙashin kansa da suka taso masa, kuma ya sanar da shugabannin jam’iyyar uzurinsa, kamar yadda ya bayyana a sanarwar da aka wallafa a shafukansa na sada zumunta.