| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Jam'iyyar NDC ta miƙa takarar shugaban ƙasa ga kudancin Nijeriya, in ji Buba Galadima
Da aka tambaye shi game da matsayar NDC a kan tsarin karɓa-karɓa na mulki tsakanin arewaci da kudancin Nijeriya, Buba Galadima ya ce, “mun miƙa takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam’iyyar NDC ga kudanci.”
Jam'iyyar NDC ta miƙa takarar shugaban ƙasa ga kudancin Nijeriya, in ji Buba Galadima
Ana ganin Peter Obi ne zai yi wa Jam'iyyar NDC takara, sannan Kwankwaso ya yi mataimakinsa / Reuters

Jam’iyyar NDC ta miƙa tikitin takarar shugaban Nijeriya na shekarar 2027 ga kudancin ƙasar, a cewar Buba Galadima, wani na hannun daman tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso

Da yake magana ranar Litinin a wani shirin siyasa na gidan talbijin na Channels, Galadima ya ce jam’iyyar NDC za ta miƙa rajistar mambobinta ga hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ranar 5 zuwa 6 ta watan Mayu.

“Da zarar mun yi wannan, mun shirya fafatawa a zaɓe,” in ji shi.

Da aka tambaye shi game da matsayar NDC kan tsarin karɓa-karɓa na mulki tsakanin arewaci da kudancin ƙasar, sai ya ce, “mun miƙa takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin jam’iyyar ga kudanci.”

Masu AlakaTRT Afrika - Hukunce-hukuncen Kotu da makomar jam'iyyun adawa a Nijeriya

Kazalika da aka tambaye shi kan ko jam’iyyar za ta zaɓi tsarin bayyana wanda ‘yan jam’iyya suka amince da shi ne, wato consensus ko kuma za ta yi zaɓen fid da gwani, sai Galadima ya ce “zaɓukan fid da gwani” su ne jam’iyyar NDC ta fi mayar da hankali a kan su a halin yanzu.

A ranar Lahadi, Peter Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP kuma wanda ya fito daga yankin kudu maso gabashin Nijeriya, da Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban Nijeriya a NNPP a 2023 suka shiga jam’iyyar NDC a hukumance.

Tun da farko Obi ya yi shelar ficewarsa daga jam’iyyar ADC, yayin da Kwankwaso ya nuna cewa yana “tuntuɓa mai faɗi” da jam’iyyar ta NDC.

Ficewarsu daga jam’iyyar ADC ta biyo bayan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ne a jam’iyyar.

Tun bayan taron duk shugabannin jam’iyyun adawa da aka yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar a ƙarshen watan da ya gabata, rahotanni sun ce Obi bai sake halartar duk wani taron jam’iyyar ADC ba.

Wasu rahotanni sun ce tsohon gwamanan na jihar Anambra bai ji daɗin cewa ba a tattaunawa batun tsarin karɓa-karɓa ba a taron.

Obi dai ya sha yin maganar tsarin na karɓa-karɓa a matakin shugaban ƙasa tun lokacin da ya shiga jam’iyyar ADC a shekarar da ta gabat , yana mai cewa gazawa wajen tattauna batun daidaito da tsarin karɓa-karɓa na raunata haɗakar da kuma haddasa rashin yarda a tsakanin masu ruwa da tsaki.