| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Kenya za ta rage farashin man dizel bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi
A cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin, Shugaban Kenya, William Ruto, ya bayyana cewa ya ba da umarnin rage farashin dizel da shilling 10 na ƙasar Kenya ($0.0772) a tsarin ƙayyade farashi na watannin Yuni da Yuli.
Kenya za ta rage farashin man dizel bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi
Jam'iyyar hamayya ce ta yi kiran a fito zanga-zangar kan ƙarin farashin mai na baya bayan nan. Hoto/Reuters / Reuters

Shugaba William Ruto ya bayyana a ranar Juma’a cewa gwamnati za ta rage farashin man dizel a ƙasar da ke Gabashin Afirka domin tallafa wa masu amfani da shi, biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan tsadar makamashi sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya.

A cikin makon nan, masu motocin sufurin na haya a Kenya sun gudanar da yajin aikin kwanaki biyu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu kusan 30. Wannan mataki ya faru ne saboda fushin jama’a kan tsadar man fetur da ta janyo tsadar rayuwa.

A cikin jawabin nasa na talabijin, Ruto ya ce ya bayar da umarnin rage farashin dizel da shilling 10 na ƙasar Kenya kwatankwacin dalar Amurka 0.0772, a tsarin farashi na Yuni zuwa Yuli domin taimakawa wajen daidaita farashin a gidajen mai da kuma kawo ƙarin sauƙi ga talakawa.

“Ta hanyar yarjejeniyar samar da mai tsakanin gwamnati da gwamnati, mun tabbatar da samun wadataccen mai duk da cikas din da ake samu a tsarin rarraba kaya na duniya, ta yadda aka tabbatar da samun mai ba tare da katsewa ba a faɗin ƙasar,” in ji Ruto.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kashe aƙalla shilling biliyan 28.1 na Kenya kan matakan rage farashin mai, kamar rage haraji, tsakanin watannin Afrilu da Yuni.

A makon da ya gabata ne Kenya ta ƙara farashin sayar da mai da kusan kashi 23.5% na tsarin farashi na watannin Mayu da Yuni, a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarancin ɗanyen mai a duniya da kuma tsadar makamashi sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya.

Rumbun Labarai
Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar
Zakuna goma sun mutu a wani gandun dabbobi da ke Tanzania
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi da lalata motocin yaƙin RSF
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Rundunar Operation Damissa a Nijar ta lalata maɓoyar mayaƙan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Dosso
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030
Majalisar Sudan ta cire 'yantawayen RSF daga tattaunawar ƙasa
An raba mutane fiye da 4,500 da gidajensu a Darfur ta Kudu da Blue Nile saboda matsalar tsaro
An ceto fiye da 'yan ci-rani 1,000 kusa da tekun yammacin Afirka cikin mako ɗaya, in ji MSF
Shugaban Zambia Hichilema ya yi farin ciki da masoyan da suka ba shi kyautar kazar gida
Gwamnatin Ghana ta kashe $4.37m don kwashe 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu
Gwamnatin Nijar ta yi kira ga jama'a su duƙufa da Al-Ƙunut domin neman tsari daga 'maƙiyan ƙasa'
Kwalara ta kashe mutum 23 a Sudan, fiye da 310 sun kamu da cutar