Fadar Shugaban Nijeriya ta ƙaryata jita-jita da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan ƙasar tare da soke amfani da dokokin Shari’ar Musulunci a jihohin arewacin ƙasar.
A wata sanarwa da Kakin Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, an bayyana cewa waɗannan kalamai ba komai ba ne illa labaran ƙanzon kurege da aka tsarar su domin haddasa ruɗani da rarraba kan al'umma, yayin da ake tunkarar zaɓukan 2027.
Sanarwar ta ce babu ƙanshin gaskiya a labarin, wanda ke cewa Shugaba Tinubu yana shirin aika ƙudirin dokar gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar zuwa majalisun dokoki domin sauya sunan Nijeriya zuwa Haɗaɗɗiyar Kasar Nijeriya, wato United States of Nigeria, a Turance.
"Babu wani shiri ko yunƙuri, na kusa ko na nesa, da shugaban ƙasa yake da shi na taɓa tsarin Shari'a a Arewa,” a cewar Bayo Onanuga.
Ta ce lamarin wani mummunan yunƙuri ne kawai na wasu ‘yansiyasa masu muguwar manufa, don fusata ‘yan ƙasa, da haifar da rikicin siyasa da dumama yanayin siyasa gabanin zaɓukan 2027.
Gwamnati ta yi kira ga ’yan ƙasar da su daina sauraron labarai marasa tushe bare makama, musamman a lokacin da ake tunkarar kakar zaɓukan 2027.














