| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Nijeriya za ta fara kwaso 'yan ƙasar daga Afirka ta Kudu saboda rikicin ƙyamar baƙi
Minist Bianca ta ce 'yan Nijeriya 130 a Afirka Ta Kudu sun riga sun nuna cewa suna son su komawa gida.
Nijeriya za ta fara kwaso 'yan ƙasar daga Afirka ta Kudu saboda rikicin ƙyamar baƙi
'Yan Afirka ta Kudu suna zanga-zangar ƙin shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, a Johannesburg, Afirka ta Kudu ranar 29 ga watan Afrilu, 2026. / AP

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fara shirye-shiryen kwaso ‘yan ƙasar daga Afirka ta Kudu yayin da ake ƙara samun tashin hankali a can wanda ke da alaƙa da ƙin jinin baƙi.

Lamarin na zuwa ne bayan jerin sabbin zanga-zanga da kuma kalaman ƙin jinin baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu, musamman a Pretoria da Johannesburg, inda masu zanga-zanga suke zargin ‘yan ci-rani da baƙin-haure da hannu a matsalolin tattalin arziki da rashin ayyukan yi da rashin tsaro da ƙasar ke fama da su.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, Ministar Harkokin wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce tuni ‘yan Nijeriya aƙalla mutum 130 suka yi rajistar komawa gida don raɗin kansu ta jiragen da gwamnati za ta bayar.

Ta ƙara da cewa tsaro da kwanciyar hankalin ‘yan Nijeriya da ke ƙaashen ƙetare su ne abu mafi mahimmaci da gwamnati ta fifita.

“Shugaban ƙasa ya sake jaddada cewa abu mafi muhimmanci a wannan lokacin shi ne tsaron ‘yan ƙasarmu. Saboda haka, ana kan shirye-shirye na tattara bayanan ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu domin hawa jiragen komawa gida cikin raɗin kansu ga waɗanda ke neman taimakon komawa gida.

“Kawo yanzu, an yi wa mutum130 rajista a ofishin jakadancinmu da ke Afirka Ta Kudu, amma ana sa rai wannan adadi zai ƙaru. Ƙungiyoyin ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu su ma suna taimaka wa ofishin jakadancinmu kan wannan batun,” in ji ta.

Ministar ta ce rashin tabbas ya ƙaru cikin ‘yan makonnin nan sakamakon zanga-zangar ƙin jinin baƙi, inda wasu ɓata-gari a Afirka ta Kudu suke far wa ‘yan Nijeriya a wasu birane.

“Akwai tashin hankali sosai sakamakon jerin zanga-zangar ƙin jinin baƙi. Shugaban Jamhuriyar Nijeriya ya nuna damuwa sosai game da lamari kuma ya yi kira ga ƙarin ƙoƙari na shawo kan lamarin daga hukumomin da lamarin ya shafa,” in ji ta.

An tabbatar da mutuwar mutum biyu

Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta tabbatar da mutuwar ‘yan Nijeriya biyu a lamura daban-daban da suka shafi jami’an tsaro.

Ta ce Amamiro Emmanuel ya mutu ranar 25 ga watan Afrilu sakamakon raunin da aka ce ya ji bayan dakarun tsaron Afirka ta Kudu sun lakaɗa masa dukai a birnin Port Elizabeth.

An ba da rahotonm cewa Nnaemeka Andrew, a cewarta, ya mutu bayan ya haɗu da ‘yansandan cikin gari na Tshwane, inda aka samu gawarsa a babban wurin ajiye gawarwaki na Pretoria ranar 20 ga watan Afrilu .

“Wannan wani abin Allah wadai ne kuma abin da ba za a lamunta ba ne. Ofishin jakadancin Nijeriya na bibiyar bincike kan waɗannan abubuwan baƙin cikin sahu da ƙafa, kuma Nijeriya na neman a tabbatar da adalci a kan waɗannan lamurran,” in ji ta.

Ministar ta kuma bayyana cewa ana tsammanin wata zanga-zanga tsakanin ranar 4 zuwa 8 ga watan Mayu, lamarin da ya sa Shugaba Bola ya ba da umarnin sa ido kan lamarin.

Nijeriya ta kuma kira jakadan Afirka Ta Kudu game da lamuran.

Ta ƙara da cewa ofisoshin jakadancin Nijeriya a Afirka ta Kudu suna cikin tuntuɓar juna da hukumomi na cikin ƙasar domin rage barazana ga ‘yan ƙasar.

Odumegwu-Ojukwu ta jaddada rawar da Nijeriya ta taka wajen taimaka wa gwagwarmayar neman ‘yancin Afirka ta Kudu, tana mai gargaɗin cewa ya zama wajibi a daina barazana ga rayuka da hajojin ‘yan Nijeriya.

“Muna jajircewa wajen aiki da Afirka ta Kudu domin neman hanyoyin kawo ƙarshen wannan yanayi na ƙin jinin baƙin,” in ji ta, tana mai cewa kwanan baya ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan kare ‘yan ƙasashen biyu.