| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Washington ta kashe dala biliyan 25 tun fara yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran - Pentagon
Jules Hurst, wanda ke rike da ayyukan mai kula da kuɗi, ya shaida wa 'yanmajalisa a yayin shaidar Kwamitin Ayyukan Sojojin Gidan Wakilai ranar Laraba cewa mafi yawan wannan kuɗin an kashe shi ne ga makamai.
Washington ta kashe dala biliyan 25 tun fara yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran - Pentagon
Washington ta kashe dala biliyan 25 tun fara yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran - Pentagon / Reuters

Yakin Amurka da Iran ya ci dala biliyan 25 zuwa yanzu, in ji wani babban jami'i na Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon, yana ba da hasashen farko na hukuma game da kuɗaɗen soja da aka kashe a rikicin duk da cewa shugaban Pentagon Pete Hegseth ya kare kasafin tsaro da aka gabatar na dala tiriliyan 1.5, yana kiran wannan gagarumin ƙari da aka samu da cewa yana da matuƙar muhimmanci don aikin "gaggawa."

Jules Hurst, wanda ke rike da ayyukan mai kula da kuɗi, ya shaida wa 'yanmajalisa a yayin shaidar Kwamitin Ayyukan Sojojin Gidan Wakilai ranar Laraba cewa mafi yawan wannan kuɗin an kashe shi ne ga makamai.

Hurst bai fayyace abin da wannan kimar kuɗin ta ƙunsa ba, ko kuma ko an haɗa cikin lissafi hasashen kashe kuɗin sake ginawa da gyaran ababen more rayuwar sansanoni a Gabas ta Tsakiya da suka lalace a martanin Iran ga wuraren Amurka da sansanoninta a ƙasashen Gulf masu haɗin guiwa.

"Za mu tsara ƙarin buƙatu na Fadar White House wanda zai zo wa Majalisa idan mun sami cikakken ƙiyasin kuɗi na wannan rikicin," in ji Hurst.

Wakilin Adam Smith, jagoran 'yan Democrat a Kwamitin Ayyukan Sojojin Gidan Wakilai, ya mayar da martani ga Hurst: "Ina farin ciki da ka amsa wannan tambaya. Saboda mun daɗe mun wannan tambayar, kuma babu wanda ya ba mu wannan adadin."

Sha'awar yaki a tsakanin Amurkawa

Amurka da Isra'ila sun fara kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, kuma a halin yanzu Amurka da Iran suna kiyaye wata dakatar da wuta mai rauni da Pakistan ta sasanta.

Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta tura dubban karin sojoji zuwa Gabas ta Tsakiya, har da ci gaba da barin manyan jiragen ruwa na yaƙi guda uku a yankin.

An kashe sojojin Amurka goma sha uku a wannan yaki, sannan ɗaruruwa sun ji raunuka.

Matsaloli a jigilar mai da iskar gas tun bayan fara yaki sun haifar da tashin farashin mai a Amurka da kuma kayan noma kamar taki, a kan dogon jerin sauran farashin kayayyakin amfani da suka tashi.

A yayin da saura watanni shida kafin zaɓen tsakiyar wa'adi inda Shugaba Donald Trump da 'yan Republican na iya fuskantar ƙalubale wajen riƙe rinjayen su a Majalisar Wakilai, 'yan Democrat na samun karɓuwa a ra'ayoyin jama'a yayin da suke ƙoƙarin danganta wannan rashin shahara ta yaki da Iran da matsalar tsadar rayuwa.

Shaharar Trump ta ragu tun bayan fara yaki.

Wani sabon binciken ra'ayin jama'a na Reuters/Ipsos ya gano cewa kashi 34 cikin 100 na Amurkawa ne ke amincewa da rikicin Amurka da Iran, daga kashi 36 cikin 100 a tsakiyar Afrilu da kashi 38 cikin 100 a tsakiyar Maris.

Rumbun Labarai
FBI za ta bayar da ladar $200,000 ga wanda ya taimaka aka kama wata sojar Amurka da ta koma Iran
Mbappe na gaba-gaba a tawagar Faransa ta Gasar Kofin Duniya; an sauƙe Camavinga, Chevalier
Xi da Trump sun amince Mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a buɗe
Amurka ta ɗauke wa magoya bayan tawagogin Afirka biyar biyan $15,000 na jinginar biza
Wani sanatan Amurka ya fada wa Majalisar Dattawa cewa ƙasar ta yi asarar jirage 39 a yakin Iran
Ƙarancin abinci: Toshe Mashigar Hormuz na barazana ga mutum miliyan 45 a duniya in ji MDD
WHO ta ce duniya ba ta fuskantar barazana bayan ɓullar cutar hantavirus a wani babban jirgin ruwa
Jamus ta waiwayi Turai bayan shirin janye sojojin Amurka
UAE ta fita daga Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin Fetur ta Duniya, OPEC
Waye zai zama Sakatare Janar na MDD? Macky Sall na fuskantar abokan takara daga Latin Amurka
Abubuwan da muka sani game da harbe-harben da aka yi a taron liyafar Trump da manema labarai
Trump ya ce harbin da aka yi ba zai hana shi samun nasara a yakin Iran ba
An fitar da Trump daga wajen liyafa da 'yanjarida yayin da 'wata kara' ta haifar da fargabar tsaro
Gagarumar gobara ta laƙume gidaje 1,000 a ƙauyen da ke kan ruwa, tare da raba dubbai da muhallansu
'Gigitaccen mahaukaci': Sanatocin Amurka sun caccaki barazanar Trump ga Iran a matsayin laifin yaƙi
Trump: Za a kai wa tashoshin lantarki da gadojin Iran hari idan ba a buɗe Mashigar Hormuz ba
Mai Bai wa Trump Shawara kan Addini tana shan raddi bayan ta kwatanta shi da Yesu Almasihu
Damuwar 'yan Republican na ƙaruwa gabanin zaɓukan rabin wa'adi saboda tasirin yaƙin Iran
Chadi za ta tura sojoji 750 domin yaƙar 'yandaban Haiti
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran