1431 GMT — Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, akalla mutum 18 ne suka mutu, da suka hada da yara hudu, yayin da wasu 60 suka jikkata, a wani harin da Isra'ila ta kai ranar Litinin a kusa da babban asibitin gwamnatin birnin Beirut.
Daraktan asibitin ya ce, sakamakon harin da Isra'ila ta kai, mai yiwuwa tarkacen manyan harsasan sun yi ɓarna a cibiyar.
Daraktan Jihad Saadeh ya kara da cewa, yayin da ba a samu asarar rai ba a cikin ma'aikatan, amma ana ci gaba da kokarin ceto mutanen a gaban asibitin.
0941 GMT — Yawan mutanen da aka kashe a yaƙin Isra'ila a Gaza ya kai 42,700
Akalla ƙarin Falasdinawa 115 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 42,718, in ji Ma’aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Wasu 100,282 kuma sun sami raunuka a cikin shekara guda, hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza - wanda ya ketare maki 100,000 - a cewar sanarwar ma'aikatar.
Ma'aikatar ta ce: "Mamayar Isra'ila ta yi kisan gilla ga iyalai bakwai a cikin sa'o'i 48 da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 115 da jikkata 487."
A halin da ake ciki, babban jami'in UNRWA Lazzarini ya ce ma'aikata a arewacin Gaza 'ba za su iya samun abinci, ruwa, kula da lafiya, da kuma warin mutuwa a ko ina ba yayin da gawarwakin da aka bari a kan tituna, karkashin baraguzai'.
0654 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 20 a arewacin Gaza
Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da sojojin Isra'ila suka kai a arewacin Gaza, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa Anadolu.
A cewar wata majiyar lafiya, Falasdinawa 12 ne suka mutu yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon luguden wuta da Isra'ila ta yi kan 'yan gudun hijira a Beit Lahia.
Shaidu sun ce jirage marasa matuka sun kewaye makarantar Khalifa Bin Zayed, inda jami'ai suka yi barazanar kashe su idan ba su tashi ba.
Wata majiyar likitocin ta ce an kashe wasu Falasdinawa takwas a harin da Isra'ila ta harba makaman atilari a yankin Al Alami da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia.
0555 GMT — Sojojin Isra'ila sun kori daruruwan Falasdinawa daga matsugunai a garin Beit Lahia da ke arewacin Gaza, tare da yi musu barazana da makamai.
A cewar rahotanni daga fararen hular da suka rasa matsugunnansu, sojojin Isra'ila da suka shafe akalla kwanaki 17 suna kai hare-hare tare da killace arewacin Gaza, sun kai samame a wata mafaka da ke kusa da asibitin Indonesiya inda Falasdinawa suka fake.
Sojojin sun tsare wani adadi mai yawa na Falasdinawa maza da ke zama a wurin.