Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada kiransa ga ƙasashen Masar da Jordan domin su karɓi Falasɗinawan Gaza da suka rasa matsugunansu, duk da cewa ƙasashen Larabawan biyu sun yi watsi da shawararsa da ke cike da ce-ce-ku-ce.
"Za su yi hakan," a cewar Trump a yayin da yake mayar da martani game da tambayar da manema labarai suka yi masa a ofisihin shugaban ƙasa a ranar Alhamis kan ƙin amincewar Masar da Jordan na kaɓar Falasɗinawa, kana ko zai yi la'akari da sanya haraji kan kowace ƙasa don tursasa su.
"Za su yi, muna yi musu abubuwa da yawa mu ma, za su yi," in ji Trump.
Kalaman na Trump na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Masar Abdel Fattah el Sisi da Sarkin Jordan Abdallah na biyu suka yi watsi da duk wani yunkuri na ƙarbar Falasɗinawan da suka rasa matsugunansu sakamakon yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza.
A makon jiya ne Trump ya yi shelar shirin "shafe" Gaza da kuma komar da Falasɗinawa zuwa wurare masu "aminci" kamar Masar ko Jordan bayan soma aikin yarjejeniyar tsaigaita wuta a yaƙin Isra'ila a ranar 19 ga watan Janairu.
Ya ce yaƙin da Isra'ila ta kwashe tsawon watanni 15 tana yi a Gaza ya mayar da yankin Falasɗinu wani ''wuri da aka ruguza''.
''Shafe Gaza''
A makon nan ne wakilin Trump na Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, ya kai wata ziyara ta ba-zata a Gaza domin nuna goyon baya ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma, kamar yadda fadar White House ta sanar, kana ta ce ya yi wata ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Bayan ziyarar Witkoff a Gabas ta Tsakiya, ya kwatanta ɓarnar da aka yi Gaza a matsayin mai munin gaske.
"Kusan babu komai da ya rage a Gaza," kamar yadda ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Axios. Ya ƙara da cewa "Mutane na koma wa matsugunansu a yankin arewa don ganin sauran abubuwan da suka rage sai kuma su juyo su bar wurin, babu ruwa, babu wutar lantarki, abin takaici ne ganin irin ɓarnar da aka haifar a wurin," in ji shi.
A matsayinsa na ɗan kasuwa da ke harkar gine-gine da hannayen-jari, ya ƙiyasta cewa za a iya ɗaukar shekaru biyar ana kwashe ɓuraguzan gine-ginen da aka lalata, sannan ana buƙatar wasu ƙarin lokuta don aikin tantance ramukan da ke ƙarkashin ƙasa kafin a soma sake yin gine-gine.
''An yi hasashen cewa, za mu iya sake gina Gaza a cikin shekaru biyar, sai dai ba abu ne mai yiwuwa ba. Wannan shiri ne da za a ɗauki shekaru 10 zuwa 15 wajen sake gina yankin.'' in ji shi.
A martaninsa na farko da ya mayar wa Trump a ranar Laraba, Shugaba Sisi ya bayyana cewa 'Zalunci ne 'raba al'ummar Falasɗinu da ƙasarsu kuma ba za mu tsoma kan ciki yin haka ba.''
Kazalika ya yi ƙari da cewa, idan har zai amince da ya ƙarbi Falasɗinawan da suka rasa matsugunansu, tabbas al'ummar Masar za su fito su yi adawa da matakin.
Haka kuma Sarki Abdallah na biyu na ƙasar Jordan shi ma ya jaddada matsayar ƙasarsa kan buƙatar barin Falasɗinawa su ci gaba da zama a ƙasarsu.
Tun a lokacin da Isra'ila ta fara yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza a watan Oktoban 2023, ƙasashen Masar da Jordan suka yi gargaɗi game da shirin shafe Falasɗinawa daga iyakokin Gaza da kuma Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
Ƙasashen duniya sun yi ta Allah wadai da shawarar Trump, inda masu suka ke bayyana hakan da ''ƙabilanci'' da kuma ''laifi na yaƙi.''
Ƙasashen Musulmai da na Larabawa da kuma Turai da ma kamar Faransa sun yi fatali da wannan shawara.