Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da wani jirgin saman fasinja ya yi karo da wani jirgin yaƙi mai saukar ungulu a sama kusa da filin jiragen sama na tunawa da Shugaba Ronald Reagan ranar Laraba da daddare inda jirgin ya faɗa cikin kogin Potoimac a wani hatsarin da aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin haɗarurrukan jiragen sama mafi muni a tarihin ƙasar.
An gano gawawwaki aƙalla 18 kawo yanzu, kamar yadda gidan talabijin na CBS ya ruwaito daga wani jami’in ‘yan sanda.
Jirgin na kamfanin American Airlines na ɗauke ne da fasinjoji 60 da ma’aikatan jirgi huɗu. Jam’ian Amurka sun ce sojoji uku ne ke cikin jirgin yaƙin mai saukar ungulu.
An dakatar da dukkanin tashi ta sauƙar jirage a filin jirgin bayan hatsarin da ya auku da misalin ƙarfe 9:00 a agogon Washington.
Jirgin na kamfanin jiragen PSA Airlines ya ci karo ne da jirgin yaƙi mai saukar ungulu samfurin Sikorsky H-60 a lokacin da yake kan hanyar isa filin jirgin saman, in ji hukumar FAA mai kula da sufurin jiragen sama a ƙasar.
"Muna sane da rahotannin da ke cewa jirgin kamfanin jiragen American Eagle mai lamba 5342, wanda kamfanin PSA ke jagoranta, da ya taso daga Wichitaa jihar Kansas (filin jirgin tunawa da Shugaba Dwitch Eisenhower) zuwa filin jirgin tunawa da Shugaba Ronald Reagan a Washington ya yi hatsari . Za mu ba da bayanai idan sun samu," in ji wani saƙon da kamfanin American Airlines ya wallafa a shafinsa na X.
An yi wa Shugaba Donald Trump bayani, in ji sakataren watsa labaransa, kuma mataimakin shugaban ƙasa JD Vance ya buƙaci mabiyansa a shafin X “su yi addu’a ga dukkan waɗanda lamarin ya rutsa da su."
Trump ya ce ya kamata “a ce an hana aukuwar hatsarin."
‘Yan sanda sun ce hukumomi da dama suna cikin masu bincike da ceto mutane a kogin Potomac wanda ke da iyaka da filin jirgin saman, amma babu bayanai nan-take game da adadin waɗanda suka mutu.
An ƙaddamar da wani jerin kwale-kwalen ceto waɗanda ake iya hura wa iska cikin kogin Potomac daga wani wuri kusa da filin jirgin saman a gefen hanyar tunawa da George Washington, arewa da filin jirgin.
Jirage masu sauƙar angulu, ciki har da na ‘yan sandan Amurka masu kula da wuraren shaƙatawa da ‘yan sandan Washington da kuma sojin Amurka, suna shawagi a saman inda hatsarin ya auku a cikin kogin Potomac.