Wani jirgin sama na ɗaukar marasa lafiya wanda ke ɗauke da wani yaro mara lafiya da wasu mutane biyar ya yi hatsari a wata unguwa a birnin Philadelphia na Amurka jim kadan bayan tashinsa.
Wani bidiyo da aka ɗauka ya nuna yadda jirgin ya fashe ya kuma kama da wuta kafin faɗuwarsa.
Kamfanin Jet Rescue Air Ambulance ya ce a ranar Juma'a mara lafiyar da wani fasinja na cikin jirgin tare da ma'aikatan jirgin hudu.
"Ba za mu iya tabbatarwa ko wani ya tsira ba,” kamar yadda kamfanin ya ce a wata sanarwa da ya fitar.
“Babbar damuwarmu a yanzu na tare da iyalan maras lafiyar , da ma’aikatanmu da iyalansu da sauran waɗanda abin ya shafa da ke wurin.”
Magajiyar garin Philadelphia Cherelle Parker ta shaida wa wani taron manema labarai cewa babu bayanai game da waɗanda suka mutu amma akwai gidaje da dama da motoci da lamarin ya shafa.
“Har yanzu ana ci gaba da bincike a wurin da lamarin ya faru,” in ji ta.
Hatsarin na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani mummunan haɗarin jirgin sama da ya faru a Amurka.
A ranar Laraba da dare, wani jirgin Amurka ɗauke da fasinjoji 60 ya ci karo da wani helikwaftan soji a birnin Washington D.C.
Duka waɗanda ke cikin jiragen sun rasu bayan hatsarin.