Kafin rasuwarsa, kotun Sweden na gudanar da bincike a kansa kan zargin tayar da hankulan ƙabilu a Sweden. / Hoto: Reuters

Wani mutum ɗan Iraƙi wanda ya sha lalata Alƙur'ani a Sweden ya mutu, kamar yadda wata kotu a Stockholm ta tabbatar a ranar Alhamis.

Kafar watsa labaran Sweden ta ruwaito cewa mutumin ya mutu ne sakamakon harbe-harben bindiga da ya rutsa da shi a wani birni da ke ƙasar.

Salwan Momika mai shekara 38, ya sha ƙona Alƙur’ani da kuma lalata shi a Sweden.

Bidiyoyin mutumin a lokacin da yake lalata Alƙur'ani sun sha bazuwa a shafukan Intanet, lamarin da ya jawo mutane da dama musamman a ƙasashen Musulmi suke harzuƙa, inda aka sha yin zanga-zanga kan hakan.

Kafin rasuwarsa, kotun Sweden na gudanar da bincike a kansa kan zargin tayar da hankulan ƙabilu a Sweden.

Wata kotu a Stockholm ta bayyana cewa an ɗaga sanar da wani hukuncin da aka yi niyyar yi a kansa a ranar Alhamis a wata shari’a wadda Momika aka gabatar da shi ƙara sakamkon rasuwar ɗaya daga cikin wanda aka gabatar da ƙara.

Alƙalin kotun da ke shari’ar Goran Lundahl ya tabbatar da cewa mutumin da ya mutu Momika ne, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Sweden TT ya ruwaito.

TRT World