Ma'aikatan lafiya a Falasdinu sun sake gano gawarwaki 20daga ƙarƙashin ɓaraguzai a Gaza / Hoto: Reuters Archive

1344 GMT — Ma'aikatan lafiya a Falasdinu sun sake gano gawarwaki 20daga ƙarƙashin ɓaraguzai a Gaza, lamarin da ya kai yawan wadanda suka mutu tun bayan fara yaƙin kisan ƙare dangi na Isra'ila a yankin a Oktoban 2023 zuwa 47,540, in ji Ma'ikatar Lafiya.

Wata sanarwa daga ma'aikatar ta ce an kuma kwantar da mutum shida da suka jikkata a asibitoci a cikin awa 24 da suka wuce, inda yawan wadanda suka ji rauni ya kai 111,618 a yaƙin cin zalin na Isra'ila.

"Har yanzu akwai mutane da ke ƙarƙashin ɓaraguzai a kan tituna a yayin da masu aikin ceto suka kasa kai wa gare su," in ji ma'aikatar.

Ta kuma ce tawagogin lafiya sun ciro gawarwaki 526 daga ɓaraguzan tun bayan da aka cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ranar 19 ga watan Janairun 2025.

1245 GMT —Kakakin kungiyar Hamas ya sanar da cewa, an fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, yana mai cewa, fifikonmu shi ne ba da mafaka da taimakon al'ummarmu, da kuma sake gina Gaza.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a tashar ta Telegram mai magana da yawun kungiyar Abdel Latif al-Qanoua ya zargi Isra'ila da "jinkirta aiwatar da ka'idojin jinƙai a yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin kisa."

Ya kara da cewa, "Matsuguni da taimakon jinƙai su ne muhimman abubuwan da suka fi muhimmanci cikin gaggawa wadanda ba za su iya fuskantar jinkirin Isra'ila ba."

Isra'ila ta ce ta aike da wata tawaga domin tattaunawa a mataki na gaba a tsagaita wuta mai rauni da kungiyar Hamas, wanda ke nuni da yiwuwar samun ci gaba gabanin ganawar firaminista Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Donald Trump a ranar Talata.

1132 GMT — Isra'ila ta tura tawaga don tattaunawar tsagaita wuta ta biyu a Qatar

Isra'ila ta ce za ta tura wata tawaga ta sasantawar zagaye na gaba a batun tsagaita wuta tsakaninta da Hamas, tana mai ba da alamar samun cigaba gabanin ganawar Firaminista Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Donald Trump.

Netanyahu zai zama shugaban wata ƙasar waje na farko da zai gana da Trumo a Fadar White House tun bayan komawarsa mulki a watan da ya gabata, kuma akwai yiwuwar zai fuskanci matsin lamba kan amincewa da tsagaita wutar da shugaban Amurkan ke ikirarin shi ya tsara.

Awanni kafin ganawar tasu, ofishin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta tura wata tawaga zuwa Doha babban birnin Qaatar nan gaba a cikin makon nan don tattaunawar.

Hamas ta ce a shirye take ta sasanta a mataki na biyu na tsagaita wutar da Qatar da Masar da Amurka ke shiryawa, wadda kuma za ta mayar da hankalu a kan samar da mafita ta dindindin ga yaƙin.

1154 GMT — Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya yi gargadi kan sake fara kai hare-hare a Gaza da Netanyahu zai yi

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bukaci kasashen duniya da su dauki matsaya guda tare da hana Netanyahu sake fara wani kisan kiyashin domin cim ma wata manufa ta siyasa.

Ya kuma bayyana cewa akwai tambayoyi a duniya game da yadda gwamnatin Netanyahu za ta kasance bayan sakin fursunonin Isra'ila.

1150 GMT — Gwamnatin Falasdinu ta kafa kwamitin da zai tafiyar da yankin Gaza bayan yakin

Gwamnatin Falasdinu ta kafa "kwamitin aiki" don kula da Gaza bayan yakin kisan kare dangi na Isra'ila.

"Gwamnatin Falasdinu karkashin jagorancin Shugaba Mahmoud Abbas ta yanke shawarar kafa wani kwamiti mai aiki da zai kula da al'amuran Gaza," in ji Firaminista Mohammad Mustafa a wani taron majalisar zartarwa.

“Gwamnati…tana kokarin gaggauta kai kayan agaji da bude hanyoyi da kawar da baraguzan gine-gine, da samar da wuraren taruwar da suka dace domin tsugunar da wadanda aka lalatar da gidajensu, a shirye-shiryen sake gina yankin.”

TRT World