Turkiyya ta jaddada ƙudirinta na faɗar gaskiya da kare halastacciyar gwagwarmayar Falasɗinawa, duk da irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe. / Hoto: TRT World

Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah wadai da abin da Ministan Harkokin Isra'ila Katz ya wallafa a baya-bayannan a kafofin sada zumunta, inda ta bayyana shi a matsayin ƙarya da yunƙurin ɓata sunan Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Turkiyya.

A wata sanarwa da aka fitar a gwamnatance, hukumomin Turkiyya sun nuna cewa Katz ba shi da wata ƙima, ko da a cikin gwamnatin Netanyahu, wacce ta shahara da irin ta'asar da take tafka wa bil adama, wacce kuma za ta bar mugun tabo a tarihi.

Sanarwar ta ce Katz yana yunƙurin nuna cewa yana da muhimmanci ne ta hanyar neman suna a wajen masu amfani da kafofin sada zumunta a Turkiyya, a wani yunƙurin kare kujerarsa a cikn abin da ta bayyana "gungun masu kisan kiyashi."

Turkiyya ta jaddada ƙudirinta na faɗar gaskiya da kare halastacciyar gwagwarmayar Falasɗinawa, duk da irin waɗannan soke-soke marasa tushe.

Gwamnatin Turkiyya ta jaddada cewa za ta ci gaba da yin tsayuwar daka a goyon bayan da take bai wa Falasɗinawa da tabbatar da adalci.

TRT World