Syria ta buƙaci tawagar Rasha da ta kai ziyara ƙasar ta mika Bashar al Assad

Syria ta buƙaci tawagar Rasha da ta kai ziyara ƙasar ta mika Bashar al Assad

Moscow ta ƙuduri aniyar ci gaba da tattaunawa don warware al'amuran da ke faruwa a Syria.
Rasha ta ce batun kare sansanonin sojinta a Syria lamari ne da ke bukatar karin shawarwari. /Hoto: AP  

Shugaban Syria Ahmed al Sharaa ya bukaci Rasha ta miƙa musu tsohon shugaban gwamnatin ƙasar Bashar al Assad wanda ya tsere zuwa ƙasar.

Wata majiyar Syria da ke da masaniya kan tattaunawar da Moscow, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba cewa, Shugaba Ahmed al Sharaa ya buƙaci Rasha ta miƙa Assad da makusantansa a yayin zaman tattaunawar da ya gudana tsakaninsa da ministan harkokin wajen Rasha Mikhail Bogdanov.

Hamɓararren shugaban na Syria, wanda ya kasance babban aminin Rasha a yankin Gabas ta Tsakiya, ya tsere zuwa birnin Moscow a shekarar da ta wuce, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin shekaru 50 da iyalan Assad suka yi a ƙasar.

Tun da farko dai, wata tawagar manyan jami'an Rasha da ta kai ziyara Syria ta bayyana goyon bayanta ga 'yancin kan ƙasar da na iyakokinta bayan hamɓarar da gwamnatin Assad, in ji ma'aikatar harkokin wajen Moscow a ranar Laraba

Tawagar Bogdanov, wanda shi ne wakilin Putin na musamman kan yankin Gabas ta Tsakiya da Afirka, ta gana da sabon shugaban Syria Ahmed al Sharaa.

"Rasha tana sake jaddada goyon bayanta ga haɗin kai da samun cikakken iko da kuma 'yanci kan ƙasar Syria," a cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ƙara da cewa ziyarar ta zo a wani ''muhimmin gaba'' a dangantakar Rasha da Syria, yayin da mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov ya bayyana ziyarar da mai ''matukar muhimmaci''.

''Ya zama wajibi a ci gaba da gudanar da tattauna wa mai ɗorewa da mahukuntan Syria, wanda kuma hakan muka sa a gaba,'' kamar yadda Peskov ya shaida wa manema labarai.

'Tattaunawa da juna'

Rasha ta ce batun kare sansanonin sojinta a Syria lamari ne da ke buƙatar ƙara tattauna wa da juna.

“Ya zuwa yanzu dai, babu abin da ya canza. Wannan batu na buƙatar wasu ƙarin tattaunawa. Mun amince da a ci gaba da zurfafa hanyoyin tattauna wa da juna,” kamar yadda Bogdanov ya shaidawa manema labarai.

A cewarsa, Rasha a bangarenta, ta jaddada buƙatar warware al'amuran da ke faruwa a Syria ta hanyar "tattaunawar siyasa da juna."

Kazalika Bogdanov ya kara da cewa, Rasha za ta yi farin cikin ganin ministan harkokin wajen Syria Asaad Hassan al Shaibani ya kai ziyara birnin Moscow.

Ziyarar tawagar Rasha ta ranar Laraba ta biyo bayan wasu ’yan kwanaki da ƙungiyar Tarayyar Turai (EU ) ta alaƙanta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Syria da janyewar sojojin ƙasashen waje daga yankunanta, inda ta buƙaci mahukuntan Syria da su sanya Rasha ta rufe sansanoninta da ke tashar jiragen ruwa ta Khmeimim da ta jiragen sama ta Tartus.

Sabbin hukumomin Syria dai ba su yanke hulɗa da Moscow ba, haka kuma ba su tilasta wa sojojin Rasha ficewa daga sansanonin Syria gaba ɗaya ba, amma a farkon wannan watan, jaridar Al Watan ta ruwaito cewa, an soke kwangilar wani kamfanin Rasha kan kula da tashar jiragen ruwa a Tartous.

Dukka sansanonin biyu na Rasha a Tartus da Khmeimim suna gaɓar tekun Bahar Rum na Syria,kuma su ne sansanin sojin Moscow da ke wajen tsohuwar Tarayyar Soviet.

TRT World