Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa a cikin Gaza, lamarin da ke sanadin mutuwar daruruwan mutane a kullum. Hoto/Getty Images / Photo: AFP

1150 GMT Mutum 7,703 hare-haren Isra'ila suka kashe a Gaza zuwa yanzu

Adadin Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a harin da ta kai zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba ya kai 7,703, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya a Gaza ta tabbatar.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai yara 3,595, in ji ma’aikatar a sanarwar da ta fitar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa Falasdinawa 19,734 aka raunata tun bayan soma wannan rikici.

Mazauna Gaza mutum miliyan 2.3 na fama da karancin abinci da karancin ruwa da magunguna sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ba kakkautawa.

1113 GMT — Sarkin Qatar da Shugaban Iran sun tattauna ta waya

Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad Al Thani da kuma takwaransa na Iran Ebrahim Raisi sun tattauna ta wayar tarho a ranar Asabar kan batun abubuwan da ke faruwa a Falasdinu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Qatar ya ruwaito.

Shugabannin biyu sun tattauna kan diflomasiyya tsakanin kasashen biyu da kuma matsalolin da ake fama da su a Gabas ta Tsakiya da sauran yankunan duniya.

Duk da cewa babu wani cikakken bayani kan abin da tattaunawar ta kunsa, amma tattaunar na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke kara tsananta luguden wuta a kan Gaza inda har ta kai ga katse hanyoyin sadarwa.

0930 GMT — Sojojin Isra'ila sun tabbatar da shiga cikin Gaza

Sojojin Isra’ila na kasa sun bayyana cewa sun shiga arewacin Gaza a cikin dare inda suka fadada ayyukansu.

Mai magana da yawun sojin Daniel Hagari ya shaida cewa har yanzu sojojin Isra’ila “na ciki”, ba tare da fadada bayanin ba.

Sojojin na Isra’ila sun kai hari ga kwamandojin Hamas a cikin dare, ciki har da shugabannin dakarun ruwa da na sama na kungiyar.

0900 GMT — Isra'ila ta lalata daruruwan gine-gine a harin da ta shafe dare guda tana kai wa Gaza

Daruruwan gine-gine ne rahotanni suka ce aka lalata a Gaza. Hoto/Getty Images

Daruruwan gine-gine Isra’ila ta lalata a arewacin Gaza a harin da ta shafe dare guda tana kaiwa, kamar yadda masu bayar da agaji suka tabbatar.

Wannan na zuwa ne bayan Isra’ila ta katse hanyoyin sadarwa a Gaza, wanda ake ganin ya zama babban cikas wurin tattara bayanai da kuma watsa labarai kan abubuwan da ke faruwa.

Babu takamaimai adadin barna da Isra’ila ta yi a Gaza a ranar Juma’a da dare da kuma irin rayukan da aka rasa, sai dai wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu ya yi gargadi kan cewa “Gaza ta soma zama makabarta ga jama’ar da yaki ya rutsa da su.”

AA
AFP
Reuters
AP
TRT World