Ganawar, idan aka tattabatar da ita, za ta iya kasancewa manuniya cewa Trump da gaske yake kan diflomasiyya da Iran / Hoto: AFP

Elon Musk, attajirin Amurka mai kusanci da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump, ya gana da jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya domin rage zaman doya da manja da ake yi tsakanin Tehran da Washington, in ji jaridar The New York Times.

Jaridar ta Ambato majiyoyin Iran ranar Alhamis suna bayyana ganawar tsakanin attajirin duniyar da Ambasada Amir Saeid Iravani a matsayin mai alamar "haske."

Mutanen biyu sun yi fiye da sa’a daya suna ganawa a wani ɓoyayyen wuri ranar Litinin, in ji jaridar.

Babu wanda ya tabbatar da ganawar tsakanin tawagar karɓar mulki ta Trump ko ofishin jakadancin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, inda ofishin jakadancin Iran ɗin ya ce ba ta da abin da za ta ce kan lamarin.

Ganawar, idan aka tabbatar da ita, za ta iya nuna alamar Trump da gaske yake game da tattaunawar diflomasiyya da Iran kuma ba ya bin tafarkin yaƙi da yawancin masu ra’ayin riƙau a jam’iyyarsa ta Republican da kuma Isra’ila ke da shi.

Za ta kuma nuna irin tasiri mai ƙarfi da Musk, mai Tesla da shafin X wanda ke kasancewa tare da Trump kusan ko ina, ke da shi inda rahotanni ke cewa attajirin na kasancewa tare da shi a lokacin da yake waya da shugabannin duniya.

Alaka mai tangal-tangal

Trump, a wa’adinsa na baya, ya wargaza yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran da aka ƙulla a ƙarƙashin Shugaba Barack Obama da ya gabace shi, maimakon hakan ya bi wata manufa ta “matsin lamba” wadda ta haɗa da ƙoƙarin hana sauran kasahen duniya sayen man Iran.

Kuma yana da hannu a kashe wani babban janar ɗin Iran Qasem Soleimani.

Rahotannin sun nuna cewa Iran ta ƙarfafa shirin inganta uranium ɗinta a lokacin Shugaba Joe Biden bayan Trump ya janye daga yarjejeniyar Obama.

Amma Trump wanda ya ayyana kansa a matsayin wani wanda ya ƙware a ƙulla yarjejeniya, a yaƙin neman zaɓensa, ya bayyana cewa yana maraba da tattaunawar diflomasiyya duk da goyon bayan da yake wa Fraministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya ba da umarnin kai hare-haren soji kan Iran bisa yaƙin Isa’ila kan Gaza.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a ranar Alhamis ya shaida wa shugaban hukumar MDD da ke kula da nukiliya cewa Tehran na son cire shakku game da shirin nukiliyar ƙasar.

Jakadin Iran ya kuma yi kira ga Musk a ganawarsu ya nemi a janye masa takunkumin Amurka domin ya iya kasuwanci a Tehran, inji jaridar Times, tana mai ambaton wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran.

TRT Afrika