Ministocin za su gana da Sakataren Harkokim Wajen Amurka Antony Blinken, sannan su gana da wakilan manyan kungiyoyin duniya da 'yan jarida. /Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai kai ziyara Washington DC babban birnin Amurka ranar Juma'a a wani bangare na amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen ganin an kawo karshen luguden wutar da Isra'ila take yi a Gaza, a cewar Ma'aikatar Harkokin Waje.

"Babban Taron Hadin-Gwiwa da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamban 2023 tsakanin Kungiyar Hada kan Kasashen Musulmai da Kungiyar Kasashen Larabawa ya amince Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya da Falasdinu da Saudiyya da Indonesia da Masar da Jordan da Qatar da Nijeriya su dauki mataki na kasashen duniya domin kawo karshen yakin Gaza da kuma samar da zaman lafiya na dindindin," in ji sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ranar Alhamis.

Ministocin za su gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, kuma za su tattauna da wakilan manyan kungiyoyin duniya da 'yan jarida.

Ranar Asabar, tawagar ministocin za ta gana da Ministar Harkokin Wajen Canada Melanie Joly a Ottawa.

Tawagar

A cikin makonni uku da suka gabata, tawagar ministocin ta gudanar da taruka a Beijing da Moscow da London da Paris da Barcelona da kuma New York. Sakatare Janar na Kungiyar Kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit yana cikin wadanda suka halarci tarukan.

A jerin tattaunawar da tawagar ta yi, ta aika da sakonni na ganin an soma samar da mafita game da rikicin — wadanda Majalisar Dinkin Duniya za ta yi aiki da su —don tabbatar da zaman lafiya na dindindin d kuma yi wa al'ummar Gaza adalci.

Kazalika ta yi kira a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta wadda Gabashin Birnin Kudus da aka mamaye zai zama babban birninta, kamar yadda iyakokinta suke a 1967.

TRT World