Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana ƙwace iko da ɓangaren Falasɗinu na kudancin Rafah da ke Gaza wanda ke da iyaka da Masar, kuma yake da matuƙar muhimmanci wajen taimakawa don fitar da waɗanda aka jikkata a yakin.
Me hakan ke nufi ga jama'ar Gaza?
A tsawon watanni bakwai da aka ɗauka ana yaƙin, mashigar Rafah da ke zaman iyaka ɗaya tilo da ba a hannun Isra'ila take ba, ta zama mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar Falasɗinawa don zuwa wata duniyar. Tana bayar da damar kai kayan taimako da kwashe mutane, da ma ɗaukar marasa lafiya daga asibitocin yankin da suka taɓarɓare.
Majiyoyin hukumomin bayar da agaji sun faɗa wa Reuters cewa an dakatar da kai kayan agaji ta iyakar Rafah.
Mahukuntan da ke kula da iyakokin da suke ƙarƙashin Falasɗinawa sun bayyana cewa rufe mashigar Rafah kamar 'Hukuncin kisa ne ga jama'ar Gaza', musamman marasa lafiya da waɗanda aka jikkata ta hanyar Rafah kaɗai ne suke iya fita daga ƙasar.
Hakazalika, an rufe mashigar da ta rage a ɓangaren kudu ita ce iyakar Kerem Shalom, wadda a baya-bayan nan aka yi amfani da ita wajen kai kayan agaji Gaza bayan harin makamin roka da Hamas ta kai, wanda ya kashe sojojin Isra'ila.
Kakakin Ofishin Ayyukan Jin kai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Jens Laerke ya ce matakin ya janyo rufe hanyoyi biyu na kai kayan agaji Gaza.
Mummunar yunwa, musamman a arewacin Gaza, na iya ta'azzara idan har aka dakatar da kai kayan agaji, in ji Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke bayar da agaji ga Falaɗinawa (UNRWA) a wata sanarwa da ta fitar ta shafin X.
Shugaban hukumar samar da abinci ta MDD ya yi gargadi kan "mummunar yunwa" a arewacin Gaza da ke da mutane miliyan 2.3.
A baya Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana damuwa game da rufe iyakar Gaza da Masar, wanda zai iya yin babban tasiri wajen samar da magunguna da kai ma'aikatan lafiya zuwa yankin Gaza.
Me ya sa wannan iyaka ke da muhimmanci??
Isra'ila ce ke iko da hanyoyin ruwa da sama na shiga Gaza da kuma mafi yawancin iyakokinta na ƙasa.
Ta kara tsaurara matakan da ta dauka a kan iyakokin tun bayan harin 7 ga Oktoba.
Bayan rufe iyakokin Isra'la, Rafah ta zama hanya daya tilo da Falasdinawa ke iya barin yankin, kuma mashigar ta zama mai muhimmanci wajen kai kayan agaji da kuma kwashe 'yan kasashen waje da marasa lafiya.
Qatar ta shiga tsakanin a tattaunawa tsakanin Masar da Isra'ila da Hamas, tare da jagorancin Amurka don bayar da dama a kwashe mutane daga yankin.
Tawagar farko ta mutanen da aka jikkata sun bar Gaza ne makonni uku bayan fara yakin a ranar 1 ga watan Nuwamba, sannan sai aka kuma kashe 'yan kasashen waje daga yankin.
Har zuwa ranar 7 ga Oktoba, Isra'ila ba ta da cikakken iko da mashigar Rafah, amma tana sanya idanu kan dukkan kai komon da ake yi a kudancin Gaza daga sansanin soji da ke Kerem Shalom. Wannan ne karo na farko da dakarun Isra'ila suka dawo iyakar Rafah tun 2005.