0715 GMT — Yarjejeniyar tsagaita wutar ta Gaza za ta fara aiki ne a ranar Lahadi da karfe 0630 agogon GMT, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari ya ce "Kamar yadda bangarorin da ke cikin yarjejeniyar da masu shiga tsakani suka shirya, tsagaita bude wuta a zirin Gaza za ta fara aiki da karfe 8:30 na safe a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, agogon kasar."
"Muna ba da shawara ga mazauna garin da su yi taka-tsantsan, kuma su jira umarni daga majiyoyin hukuma."
2200 GMT — Shugabannin Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun ce a shirye suke su mulki Gaza
Shugabanin Falasdinu da ke kula da wasu sassan Yammacin Gabar Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, sun ce a shirye suke "su rinƙa kula da lamura" a Gaza, a cewar wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito.
Ofishin shugaban kasar Mahmud Abbas ya ce hukumomin gudanarwa da tsaro na hukumar Falasdinu sun kammala shirye-shiryen maido da muhimman ayyuka a Gaza da Hamas ke mulki.
Sai dai har yanzu babu wani shiri na wanda zai mulki Gaza bayan yakin kisan kare dangi na Isra'ila.