Ma’aikatar shari’a ta Isra’ila ta saki sunayen Falasɗinawa 95 da za a saki ranar Lahadi sakamakon aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Sunayen sun ƙunshi na mata da matasa da suka kai har shekara 25.
Daga cikin matan da za a saki akwai Dalal al Arouri, ‘yar’uwar Saleh al Arouri, mataimakin shugaban Hamas wanda Isra’ila ta kashe a watan Janairun bara.
Sunayen sun kuma ƙunshi na wata ‘yar jarida Bushra al Taweel, wacce aka saki a musayar fursunoni da aka yi a baya a 2011 tsakanin Hamas da Isra’ila. ‘Ya ce ga wani babban jagoran Hamas Jamal al Taweel wanda ya taɓa zama magajin garin birnin Al Bireh da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.
Khalid Jarrar, fitaccen jagoran wata ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa mai ra’yin gurguzu PLFP kuma wakili a Majalisar Dokoin Falasɗinawa, shi ma yana cikin waɗanda za a saki.
A yanzu haka akwai Falasɗinawa 10,400 a gidajen yarin Isra’ila, da suka haɗa da mutanen da aka kama a Gaza lokacin yaƙin da Isra’ila ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza, kamar yadda Hukumar Falasɗinawa mai Kula da Walwalar Waɗanda aka Tsare da Kuma Ƙungiyar Fursunoni ta Falasaɗinawa su faɗa.
An tsare su gomman shekaru
Wasu daga cikinsu sun yi shekaru da dama a gidajen yarin Isra'ila.
A shekarar 2004 ne wata kotun sojin Isra'ila ta yanke wa Abdallah al Barghouti hukuncin ɗaurin rai da rai har sau 67, saboda samunsa da hannu a wasu hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai a shekarun 2001 da 2002, wanda ya yi sanadin mutuwar Isra'ilawa da dama.
An kama Ibrahim Hamed, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai har sau 54 a shekarar 2006 a Ramallah. Ya kasance cikin jerin mutanen da Isra’ila ke nema ruwa a jallo tsawon shekaru takwas kafin a kama shi. Isra'ila ta tsare matarsa tsawon watanni takwas sannan a shekarar 2003 ta rushe gidansa.
An haifi Nael Barghouti a shekara ta 1957, ya shafe shekaru 44, ko kashi biyu bisa uku na rayuwarsa na shekaru 67, a tsare a hannun Isra'ila - fiye da kowane Bafalasdine. A shekarar 1978 ne aka ɗaure shi a gidan yari a karon farko bayan da ya taka rawa a harin da ya kashe wani sojan Isra'ila a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye. An fara sako shi a shekara ta 2011 a ƙarƙashin wata yarjejeniya.
Bayan da aka sake shi a shekarar 2011, ya auri Eman Nafe, wadda ita ma ta shafe shekaru 10 a gidan yari a Isra'ila. Isra'ila ta sake kama Barghouti a 2014.
Hassan Salama, an haife shi a sansanin yan gudun hijira na Khan Younis na Gaza a 1971, an yanke masa hukunci a 1996. An yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai har sau 48.
Marwan al Barghouti jigo ne a ƙungiyar Fatah, ana kallon Barghouti a matsayin wanda zai gaji Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas. An kama shi a shekara ta 2002, kuma an yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a shekara ta 2004.
Sojojin Isra'ila sun kama Ahmed Saadat shugaban ƙungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine (PFLP) a shekara ta 2006. An yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 30 a gidan yari a shekara ta 2008.