Tashar talabijin ta Indiya ta ce 'yan sanda a babban birnin kasuwanci na Mumbai sun tsare, kuma suna tuhumar wanda ake zargi da kai hari da wuƙa da daddare kan jarumin Bollywood, Saif Ali Khan, amma 'yan sandan ƙasar ba su tabbatar da tsare mutumin ba.
An caka wa Khan mai shekara 54 wuƙa sau shida a lokacin da aka yi ƙoƙarin kutsawa gidansa a unguwar da yake zaune da safiyar ranar Alhamis.
Gidan talbijin na India Today da sauran su sun nuna 'yan sanda na tisa ƙeyar wani mutum da ke sanye da farar riga zuwa cikin caji ofis sannan suka gabatar da shi a matsayin wanda ake zargi da aikata laifin.
Likitocin da suka yi masa tiyata a ɓargonsa da wuya da hannaye sun ce ba ya cikin hatsari.
Sai dai jami’in ‘yan sanda Dikshit Gedam bai tabbatar da tsare mutumin ba, a maimakon haka ya ce babu wani ci gaba da aka samu a binciken.
"Babu wani bayani daga jiya game da abin da muka fada," Gedam, babban jami'in binciken, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A ranar da ta gabata ‘yan sanda sun ce sun gano wanda ya yi yunkurin fashi da makamin tare da kaddamar da bincike a kansa.
Samun sauƙi bayan tiyata
Khan, mai shekaru 54, daya daga cikin fitattun taurarin Bollywood, wanda ya fito a fina-finai da shirye-shiryen talabijin da dama, ya shiga asibitin kayan jikinsa sun rine da jini, tare da dansa Taimur mai shekaru shida.
Niraj Uttamnani, daya daga cikin likitocin da suka yi wa Khan tiyata, ya shaida wa manema labarai cewa, "idan da wuƙar ta ƙara shiga jikinsa sosai, da sai ya ji rauni a ɓargon ƙashin bayansa, inda ya kara da cewa jarumin ya yi sa'a wuƙar ba ta shiga da zurfi ba.
"Ya yi matuƙar sa'a."
Wani likita, Nitin Dange, ya kara da cewa, "Yana iya tafiya, kuma yana samun sauƙi." Harin da aka kai wa Khan, wanda dan tsohon kyaftin din wasan kurket ne na Indiya Mansur Ali Khan Pataudi da jaruma Sharmila Tagore, ya girgiza masana'antar fim da mazauna birnin, inda da yawa daga cikinsu suka yi kira da a inganta tsaro.
A wata sanarwa da ta fitar a dandalin sada zumunta, matar Khan, Kareena Kapoor Khan, ta bukaci kafafen yada labarai da su daina yaɗa jita-jita a kan lamarin.
"Ta kasance rana ce mai ban da tashin hankali ... kuma har yanzu muna nazarin abubuwan da suka faru," 'yar fim din mai shekaru 44 ta fada a shafinta na Instagram.
Ma'auratan suna da 'ya'ya biyu maza, baya ga 'ya'yan Khan guda biyu daga aurensa na baya.