Majalisar Tsaron Isra'ila ta amince da tsagaita wutar da zai dakatar da yaƙin da take yi da Hamas a Gaza tare da sakin fursunonin da dukkan ɓangarorin biyu ke tsare da su.
A yanzu yarjejeniyar za ta je gaban majalisar a cike.
Ofishin firaminista ya ce idan aka cim ma yarjejeniyar, to tsagaita wutar za ta fara aiki a ranar Lahadi da zarar an saki kashin farko na fursunonin.
TRT World