Shafukan intanet na ‘yan adawa a ƙasar a baya sun rinƙa alaƙanta Alƙali Moghiseh a matsayin wanda ke da hannu a shari’ar da aka yi ta fursunonin siyasa a ƙasar. / Hoto: Others

An harbe wasu alƙalai biyu na Kotun Ƙolin Iran a Tehran babban birnin ƙasar a ranar Asabar sannan an jikkata wani alƙali ɗaya, kamar yadda shafin watsa labarai na Mizan a ƙasar ya ruwaito.

Rahotanni sun ce maharin ya kashe kansa bayan ya buɗe wuta kan alƙalan a wajen Kotun Kolin ƙasar.

Kafar watsa labarai ta Iran ta ce wani dogarin ɗaya daga cikin alƙalan shi ma ya tsira da raunuka.

Zuwa yanzu dai babu tabbaci kan dalilin kai harin.

Sashen shari’a na ƙasar ya bayyana alƙalan da aka kashe inda ya ce su ne Hojjat al-Islam Razini da Hojjat al-Islam Muslimeen Moghisheh

Shafukan intanet na ‘yan adawa a ƙasar a baya sun rinƙa alaƙanta Alƙali Moghisheh a matsayin wanda ke da hannu a shari’ar da aka yi ta fursunonin siyasa a ƙasar.

TRT Afrika da abokan hulda