An tabbatar da mace Musulma ta farko a matsayin mai shari’a a babbar kotun Amurka

An tabbatar da mace Musulma ta farko a matsayin mai shari’a a babbar kotun Amurka

A baya Choudhury ta yi aiki a matsayin darakta a wata Kungiyar Kare Hakki ta Fararen Hula ta ACLU.
A yanzu za ta zama Mai Shari’a a Gundumar Gabashin New York. Hoto: AA

Majalisar Dattijan Amurka ta tabbatar da mace Musulma ta farko Nusrat Jahan Choudhury a matsayin mai shari’a a babbar kotun tarayya ta kasar.

Nusrat, wadda Ba’amurkiya ce ‘yar asalin Bangladesh ta kai labari da kyar a kuri’ar da sanatocin suka kada, inda ta samu mutum 50 suka zabe ta, yayin da 49 suka ki zabarta.

A yanzu za ta zama Mai Shari’a a Gundumar Gabashin New York.

A baya Choudhury ta yi aiki a matsayin darakta a wata Kungiyar Kare Hakki ta Fararen Hula ta ACLU.

An bayyana ta a matsayin wacce ta jagoranci yaki da nuna wariya a lokacin da take aiki a kungiyar.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattijan Chuck Schumer ya jinjina wa wannan nasara ta Choudhury, yana mai cewa yana alfaharin gabatar da ita ga Shugaba Joe Biden da ba shi shawarar ya yi aiki da ita.

“Ta kafa tarihi wajen zama Ba’amurkiya ‘yar asalin Bangladesh ta farko da ta zama alkaliya a kotun tarayya,” ya rubuta a Twitter.

Kungiyar ACLU ma ta wallafa sakon taya murna a Twitter inda ta ce “Nusrat kwararriyar lauya ce da ta kware a kare hakkin dan adam.

Sai dai Manchin, wanda shi ne sanata daya jal na Jam’iyyar Democrat da bai kada wa Choudhury kuri’a ba, ya ce “wasu daga cikin kalaman da ta taba yi a baya na bukatar a binciki irin halayyar bambanci tata da ta dinga nuna wa hukumomin tsaronmu.”

AA