Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

0700 GMT — Aƙalla Falasɗinawa takwas waɗanda suka haɗa da mata biyu da yara biyar Isra'la ta kashe a wani sabon hari ta sama da ta kai wata makaranta ɗauke da farar hula a tsakiyar Gaza.

An kashe wata uwa da 'ya'yanta huɗu haka kuma an jikkata wasu a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai gidan iyalin Al-Samak da ke birnin Deir al Balah, kamar yadda hukumar kare farar hula ta Gaza ta tabbatar.

A wata sanarwa ta daban, hukumar kare farar hulan ta kara da cewa harin da Isra'ila ta kai kan makarantar Khaled Bin Al-Waleed da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Nuseirat, ya kashe wani mutum, matarsa, da 'yarsu, tare da jikkata wasu.

0630 GMT — Gomman hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama a kudanci da gabashin Lebanon sun yi sanadin mutuwar aƙalla farar hula ɗaya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NNA ya tabbatar.

“Jiragen yaƙin maƙiya sun ƙaddamar da hare-hare....sama da hare-hare 80 a cikin minti 30”, inda suka afka gundumar Nabatiyeh da ke kudancin Lebanon,” in ji kamfanin dillancin labaran na Lebanon.

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare tsakanin mayaƙan Hezbollah na Lebanon da kuma sojojin Isra’ila.

TRT Afrika