0841 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 17 Isra’ila ta kashe tare da jikkata wasu gommai a wasu sabbin hare-hare da ta kai Gaza, kamar yadda majiyoyin kiwon lafiya suka tabbatar.
Mutum shida ne suka rasa rayukansu sannan da dama suka jikkata a wani hari da Isra’ilar ta kai makarantar Kafr Qasim, inda dubban farar hula waɗanda suka rasa matsugunansu suka samu mafaka a sansanin Shati da ke yammacin Gaza, kamar yadda wata majiya ta kiwon lafiya ta tabbatar.
Haka kuma akwai ƙarin mutum huɗu da suka rasu sai 15 suka jikkata a wani harin da Isra’ila ta kai a wani gida da ke Deir al Balah, kamar yadda majiyar ta ƙara da cewa.
Wata majiyar kiwon lafiya ta ce wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gida ya kashe karin mutane hudu a arewacin Rafah da ke kudancin Gaza.
Likitoci sun ce an kashe karin mutane biyu a wani hari da aka kai a garin Khuza'a da ke gabashin Khan Younis a kudancin Gaza.
0500 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki fiye da 100 zuwa cikin kasar daga Lebanon, inda wasu suka sauka a kusa da birnin Haifa.
Masu mayar da martani na farko na Isra'ila sun ce hare-haren da aka kai a safiyar Lahadi sun yi sanadin jikkata aƙalla mutum uku a kusa da Haifa tare da lalata gidaje da cinna wa motoci wuta.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun saka hotunan rokokin da Isra'ila ta harbo daga arewacin ƙasar domin daƙile waɗanda aka harbo cikin ƙasar, inda aka yi ta bayar da rahotanni dangane da ƙarar fashewar abubuwa da aka rinƙa ji.
Haka kuma kafofin watsa labarai na Isra'ila sun bayyana cewa harin baya-baya da Hezbollah ta kai ya faɗa kan filin jirgin Ramat David da ke kusa da Haifa.
0416 GMT — Hezbollah ta bayyana cewa adadin mambobinta da suka rasu sakamakon rikicin da ta fara da Isra’ila tun daga 8 ga watan Oktoba ya kai mutum 501.
Ƙungiyar ta Lebanon ta bayyana cewa adadin mambobinta da aka kashe a sa’o’i 24 da suka gabata ya ƙaru zuwa 17 bayan rasuwar Muhammad Hussein Ubeid da kuma Abbas Mahmoud Salih.
A halin yanzu ana ci gaba da fafatawa tsakanin Hezbollah ɗin da kuma sojojin Isra’ila.