Dakarun Isra'ila sun kai samame ofisoshin tashar talabijin ta Aljazeera da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye da sanyin safiyar Lahadi, inda suka ba da umarnin rufe ofishin a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da matsa lamba kan gidan talabijin ɗin na Qatar, a yayin da yake ba da labarin mummunan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Al Jazeera ta watsa hotunan sojojin Isra'ila kai tsaye a tasharta ta harshen Larabci suna ba da umarnin rufe ofishin na tsawon kwanaki 45.
Matakin dai shi ne karo na farko da Isra'ila ke rufe wata kafar yada labarai ta ketare da ke aiki a ƙasar.
Sai dai duk da haka, Al Jazeera na ci gaba da gudanar da ayyukanta a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye da kuma Gaza.
Al Jazeera ta yi Allah wadai da matakin yayin da take ci gaba da yada shirye-shiryenta kai tsaye daga birnin Amman a makwabciyar kasar Jordan.
Sojojin Isra'ila dauke da makamai sun shiga ofishin kuma sun shaida wa masu watsa labarai kai tsaye cewa za a rufe tashar na tsawon kwanaki 45, yana mai cewa akwai bukatar ma'aikatan su fice cikin gaggawa.
Daga baya cibiyar sadarwa ta watsa wani abu da ake ganin sojojin Isra'ila ne suna yayyaga tuta a wata baranda da ginin da ofishin Aljazeera ke amfani da shi.
Al Jazeera ta ce tutar tana dauke da hoton Shireen Abu Akleh, wata 'yar jarida Bafalasdiniya Ba'amurkiya da sojojin Isra'ila suka harbe a watan Mayun 2022.
'Hukuncin soji na son rai'
"Akwai hukuncin kotu na rufe gidan talabijin na Al Jazeera na tsawon kwanaki 45," kamar yadda wani wani sojan Isra'ila ya fada wa shugaban ofishin Al Jazeera Walid al-Omari, a lokacin da ake watsa labarai kai-tsaye. "Ina umartarka da ku dauki dukkan kyamarori ku bar ofis ɗin yanzu."
Daga baya Al-Omari ya ce sojojin Isra'ila sun fara kwashe takardu da kayan aiki a ofishin, yayin da ake iya ganin hayaƙi mai sa hawaye ake kuma jin ƙarar harbe-harbe a yankin.
Kungiyar 'yan jarida ta Falasdinu ta yi Allah-wadai da farmakin da Isra'ila ta kai.
"Wannan hukunci na soji ba bisa ka'ida ba wani sabon zalunci ne ga aikin jarida da kafofin yada labarai," in ji ta.
Tun daga ranar 7 ga Oktoba ne gidan talabijin din yake watsa labaran yaƙin Gaza ba ƙaƙƙautawa, kuma ya ringa watsa shirye-shiryensa tsawon sa’o’i 24, a daidai lokacin da Isara’ila ke zafafa kai hare-hare ta ta ƙasa, wanda ya kashe ya kuma jikkata ma’aikatanta.
Yayin da take ba da rahotanni da suka hada da mutanen da yaƙin ya rutsa da su suka mutu ko suka jikkata daga tushe, a wani lokacin Aljazeera Arabic tana wallafa bidiyon sanarwa daga Hamasa da sauran jagorori a yankin.
Hakan ya haifar da ikirarin Isra'ila tun daga jami'ai har zuwa Firayiminista Benjamin Netanyahu na cewa tashar "ta cutar da tsaron Isra'ila tare da tunzura mutane su yi wa sojoji bore." Aljazeera ta musanta wannan ikirari da kakkausar murya, wacce babbar mai ɗaukar nauyinta Qatar, a kasance muhimmiya mai shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da kawo karshen yakin.
An sha ba da umarnin rufe tashar talabijin ta Al Jazeera a Isra'ila tun daga lokacin, sai dai a baya ba a taɓa ba da umarnin rufe ofisoshin tashar a Ramallah ba.
Rufe ofishin na gidan talabijin ɗin na Aljazeera na Ramallah ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna fargaba dangane da yiwuwar fadadar yaki zuwa Labanon, inda na'urorin sadarwa suka fashe a makon da ya gabata, a wani yunkuri na yin zagon kasa da Isra'ila ta yi kan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.