A cikin kwanaki biyun da suka gabata an yi ruwan sama ba kakkautawa a Kolkata, babban birnin jihar Bengal ta Yamma ta Indiya. Amma hakan bai hana kungiyar Likitoci ta West Bengal Junior da 'yan kasa daga kowane bangare na rayuwa shiga zanga-zangar neman a yi adalci ga likitar da aka yi wa fyade aka kashe a Kwalejin Kiwon Lafiya ta RG Kar a watan da ya gabata ba.
Sama da kwanaki 36 kenan da aka kashe likitar a daya daga cikin tsoffin kwalejojin likitanci a kasar. Tun daga lokacin ne zanga-zangar ta barke a birnin Kolkata, inda masu zanga-zangar ke neman a yi musu adalci, inda hakan ya jawo nasarar korar kwamishinan 'yan sandan birnin da jami'an lafiya na gwamnatin jihar.
Mutane sun nuna bacin ransu a ko ina cikin kasar, da kuma birane 25 na Turai da Arewacin Amurka.
A cikin jawabin ranar samun ‘yancin kai a watan da ya gabata, Firaminista Narendra Modi ya yi ishara da wannan aika-aika, yana mai cewa ya kamata gwamnatocin jihohi su sanya tsoron hukunci a zukatan wadanda suka aikata laifin tare da kara kwarin gwiwa a cikin al’umma. Sai dai, da alama shi ma jam'iyyarsa ta BJP tana fama da matsalar fyade da kanta.
Duk da haka, abin da ya faru a daren ranar 9 ga watan Agusta, ba wai kawai ya bude kofofin fushi ba, har ma ya fama tsohon gyamboa, wanda ya tilasta wa Indiyawa sake yin tambayoyi masu tsanani game da batun fyade, matsalar da ta dade a cikin al'ummarmu.
A cikin watan da ya gabata, manyan al'amura da dama sun faru a Indiya.
Na daya, Kotun Kolin Indiya ta fara sauraron shari'ar Kolkata, kuma Hukumar Bincike ta Tsakiya (CBI) ta dauki hurumin shari'ar.
A halin da ake ciki, wata kotun gundumar Siliguri (a Arewacin Bengal) ta ba da sanarwar yanke hukunci kan wani shari’ar fyade da kisan kai da ya faru a Matigara na yankin Siliguri, kusan shekara guda da ta wuce. An yanke wa wanda ya aikata laifin hukuncin kisa.
Bugu da ƙari kuma, ana ci gaba da samun karin wasu laifukan fyade a fadin kasar, ciki har da fyade da aka yi wa wata mata da rana a garin Ujjain da ke Madhya Pradesh, da kuma fyade da kisan wata yarinya Dalit mai shekaru 14 a Bihar, da kuma rahotanni da ke cewa ma'aikatan wata makaranta sun yi lalata da daliban nazire biyu ('yan mata) a Badlapur, Maharastra.
Kuma wadannan su ne kawai abubuwan da suka bayyana a kanun labarai.
Daga duk waɗannan abubuwan da suka faru a lokaci ɗaya, yana da kyau a saddaƙar cewa Indiya tana cikin wani yanayi mai sarƙaƙiya, mai ban tsoro inda abubuwa biyu suka tabbata.
Na daya, cewa ana aiwatar da tsarin bin doka, bangaren shari'a na kokarin tabbatar da adalci, kuma ana yanke hukunci da aaiwatar da shi. Na biyu, ana ci gaba da cin zarafin mata da kuma yi musu fyade.
To mece ce matsalar, kuma me yasa Indiya ba za ta iya gyarawa ba?
Ƙoƙarin sauyawa
A ranar 16 ga Disamban 2012, wasu mutane shida sun yi gangamin yi wa wata daliba 'yar shekara 23 fyade a cikin wata motar bas mai motsi a New Delhi.
Matar da aka yi wa fyaɗen da ake yi wa laƙabi da Nirbhaya, ko kuma Marar Tsoro, a rahotannin kafafen yada labarai saboda dokar Indiya ta hana bayyana sunan wanda aka yi wa fyade, ta mutu ne kwanaki bayan harin.
Laifin dai laifi ne na cin zarafi da ya girgiza kasar, wanda ya haifar da cece-ku-ce na tsawon watanni, tare da janyo hankulan kasashen duniya da haifar da sauye-sauye, ciki har da bullo da wata sabuwar dokar yaki da fyade wadda ta sanya hukuncin kisa ga masu laifin.
Mutanen hudu da aka samu da laifi an yanke musu hukunci kuma an rataye su a ranar 20 ga Maris din 2020 a gidan yarin Tihar. Na biyar ya kashe kansa ne a lokacin da yake zaman yari na hukuncin da aka yanke masa, sannan kuma an saki mafi karancin shekaru a cikin masu laifin wanda bai kai shekara 18 ba a lokacin da aka aikata, bayan da ya shafe wa'adin shekaru uku, hukunci mafi yawa a karkashin dokar kananan yara a Indiya.
A cikin 2018, wata mummunar shari'ar ta fito fili: fyade da kisan karamar yarinya (yara) a Indore, Madhya Pradesh. Wannan ya haifar da shari'a cikin gaggawa ta tsawon makonni uku, wadda ita ce mafi sauri da aka taba yi a shari'ar fyade a Indiya bayan samun 'yancin kai, tare da mai laifin mai shekaru 26 da aka samu da laifi kuma aka yanke masa hukuncin kisa.
Saƙonnin da aka aika ta cikin shari'o'in biyu suna da ƙarfi kuma a bayyane suke, amma abubuwan da suka shafi lalata, fyade da kisan kai suna ci gaba da yaɗuwa tsawon shekaru.
Idan aka koma wata uku na kashi ukun wannan shekara, an bayyana hukunce-hukuncen shari'a da dama da kuma yanke hukunci, ciki har da hukuncin kisa, kuma za a iya aiwatar da su duka.
A ƙasar da tsarin shari'a ke ɗaukar shekaru, ana maraba da hukunci kuma yana saka kyakkyawan fata.
Duk da haka, har yanzu ba a kai ga ainihin gaskiyar ba. Bayanai na kasa da kasa da na Indiya sun bayyana wani jadawali da ake samu na cin zarafin mata da suka hada da fyade da kisa. Ka yi la'akari da shekaru uku da suka gabata kaɗai.
A cewar rahoton Hukumar Laifuka ta Kasa (NCRB), wanda ya fitar da kididdigar laifuka na 2022 a karshen shekarar 2023, Indiya ta sami karuwar kashi 4 cikin 100 na laifukan cin zarafin mata da suka hada da fyade, kisan kai, mutuwa sakamakon daura aure da cin zarafi da watsa ruwan asid.
A shekarar 2020, an sami rajistar laifuka 371,503 na cin zarafin mata. Tun daga wannan lokacin, an sami ƙaruwa mai ban tsoro a cikin adadin laifuka tare da ƙididdigar 445,256 a cikin 2022.
Laifukan fyade da aka yi rajistarsu a shekarar 2021 sun kai 31,677, ko kuma matsakaita na shari'o'i 87 a rana - inda aka samu karuwar kashi 19.34 daga shekarar 2020. Musamman ma, laifukan da suka shafi fyade da aka rubuta tsakanin 2018-2022 sun tsaya ne kawai da kashi 28 cikin 100.
A shekarar da ta gabata, Cibiyar Mata, Zaman Lafiya da Tsaro ta Georgetown ta sanya Indiya a kasa ta 128 daga cikin 177 cikin jerin kasashe masu rauni ta fannin tsaron mata da adalci shigar da mata cikin al'amura.
Dokoki
To me Indiya ke yi a kan wannan matsala ta fyade?
A farkon wannan shekarar, West Bengal ta zartar da Dokar Aparajita. Dokar ta gabatar da sabbin tanadi da suka shafi laifukan cin zarafi, gami da fyade. Kudurin dokar na da nufin kara karfafa kare yara da mata a yammacin Bengal.
Sauran jihohin dai na kokarin samar da dokoki bisa layukan da suka dace, kuma kotuna a fadin kasar na kara zafafa kokarin ganin an yi adalci.
To amma me yasa har yanzu fyade ya kasance daya daga cikin laifuffukan da ake yi wa mata a Indiya? Me yasa Indiya ke fafutukar dakile al'adar fyade? Amsar ba layi daya ba ce.
A cikin ƙasa mai rarrabuwar kai, fyade yana nufin fiye da laifin cin zarafi da aka keɓe. Wani makami ne na daukar fansa a cikin siyasar kabilanci.
Wannan ya dawo mana da muguwar dabi’ar mamayar maza da ƙin jinin mata ta Indiya, inda a nan ne cin zarafi da azabtar da mata ya halatta kuma ana kunyatar da mata saboda fyade.
Idan aka yi la'akari da wannan aibi na al'umma, da wuya adadin fyade ya ragu ko kuma a daina gaba daya.
Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa hukunce-hukuncen tarihi kamar na Nirbhaya ya kasa haifar da wani canji na gani.
Hakan ya nuna rashin tsoron doka, saboda hukuncin daurin rai da rai ko hukuncin kisa ba sa tsorata masu laifi.
Da yake ba a daukar darussan da suka gabata da muhimmanci ba, ba za a iya kafa al'adar da ke ƙalubalantar mamayar maza ba.
Bugu da ƙari, akwai raguwar rahoton 'yan sanda da yin rajistar korafe-korafe, da ke hana saurin aiwatar da dokokin da ake da su na yaƙi da laifukan cin zarafi.
Tafiya ce mai nisa zuwa ga al'adar samun ƙima wacce a ƙarshe za ta iya doke ɗabi'a, ɗabi'a mai guba da rashin fahimta a Indiya.
Yayin da zanga-zangar Kolkata ta kai kololuwa, lokaci ya yi da za a koyi darusi daga abubuwan da suka faru a baya don wargaza babbar matsalar laifukan cin zarafi a kowane mataki na zamantakewa.
Ko akwai fatan cewa Indiya za ta farka daga wannan cutar mantuwar!
Nilosree BiswasNilosree Biswas is an author and filmmaker who writes about history, culture, food and cinema of South Asia, Asia and its diaspora.
Nilosree BiswasNilosree Biswas marubuciya ce kuma mai shirya fina-finai da ke yin rubuce-rubuce game da tarihi, al'adu, abinci da sinima na Kudancin Asiya, Asiya da al'ummominsu na ƙasashen waje.