Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024
0945 GMT –– Dakarun Isra'ila sun kai hari a kudancin Beirut bayan hukumomi sun bayar da umarni ga mazauna yankin su bar wuraren, a yayin da mahukuntan Isra'ila suke shirin yanke shawara kan yiwuwar ƙulla yarjejeniyar tsagaita da mayaƙan Hezbollah na Lebanon.
Wani makamin roka da aka harba daga Lebanon ya yi mummunar ɓarna a matsugunan Isra'ila na arewacin Isra'ila, a cewar kafofin watsa labaran ƙasar.
Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta ce mayaƙan Hezbollah sun harba rokoki biyar daga Lebanon zuwa Upper Galilee a arewacin Isra'ila.
A cewar kafar watsa labaran, makamin roka ya faɗa kan wani gini a yankin Kiryat Shmona, inda ya yi mummunar ɓarna.
1522 GMT —Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 11 a sabon harin da ta kai a Birnin Gaza
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla tare da jikkata gommai a hari da ta kai da makaman atilari a yankin Gaza.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito cewa Isra'ila ta kashe mutum shida, ciki har da mata da ƙananan yara tare da jikkata gommai a hari ta sama da ta kai a gidan Jadba a kusa da Masallacin Al Rahma da ke yankin Zarka a Al Tuffah, area maso gabashin Birnin Gaza.
Tun da farko, sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa biyu tare da jikkata wasu a harin makaman atilari da suka kai a Layin Kashku da ke yankin Abrar na gabashin Al Zaytoun da ke kudu maso gabashin Birnin Gaza.
Bugu da ƙari, dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa uku tare da jikkata wasu a hari ta sama da suka kai kan wasu mutane a sansanin 'yan gudun hijira na Al Shati da ke yammacin Birnin Gaza.
A tsakiya Gaza, wani jirgi mara matuƙi na Isra'ila ya kashe wani Bafalasɗine a sansanin 'yan gudun hijira na Al Bureij. Masu aikin ceto sun kasa fito da gawarwakin da suka maƙale a ƙarƙashin ɓuraguzai a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a yankin.
A kudancin Gaza, motocin sojojin Isra'ila sun buɗe wuta da mashin gn a yankin arewa maso kudancin Mawasi Rafah.
Ƙarin labarai 👇
2330 GMT — Wani ɗan majalisar dokokin Lebanon ya ce an kusa ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila
An kusa kammala ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Lebanon da Isra'ila kuma nan da awanni 36 komai zai tabbata idan ba a samu akasi ba, a cewar wani ɗan majalisar dokokin Lebanon
"Halin da ake ciki yana da ƙarfafa gwiwa, kuma yarjejeniyar tsagaita wuta tana dab da kammala. Nan da awanni kaɗan masu zuwa za a kammala ta sannan a fitar da sanarwa idan komai ya tafi kamar yadda aka tsara," in ji ɗan majalisa Qassem Hashem a hira a Anadolu Agency.
Bayanin nasa ya yi daidai da wani rahoto da ke cea jami'an tsaron Isra'ila dza su gana ranar Talata kan batun cim ma matsaya da ƙungiyar Hezbollah.