Lebanon / Hoto: AP

Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024

1423 GMT — Akalla mutum 11 ne suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata a wasu jerin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a kudanci da gabashin Lebanon, in ji ma'aikatar lafiya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, wani yajin aikin da aka yi a garin Maarakeh da ke kudancin kasar ya yi sanadin mutuwar mutum takwas da jikkata hudu, ciki har da guda daya mai tsanani.

Kamfanin dillancin labarai na NNA ya rawaito cewa, wani harin da aka kai ta sama kan wani gini a Ghaziyeh a kudancin kasar Lebanon, ya yi sanadin mutuwar wasu mutum biyu.

NNA ta bayyana cewa, an kashe wani mutum daya bayan da jiragen yaki suka sake kai wani hari a lardin Baalbek-Hermel da ke gabashin kasar Lebanon.

Hakazalika jiragen yakin Isra'ila sun sake kai hare-hare ta sama a yankin kudancin birnin Beirut, sai dai kawo yanzu babu wani bayani game da asarar rayuka.

1016 GMT –– Rasha ta nemi a kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila kan fararen hula a Lebanon

Fadar Kremlin ta ce Rasha ta yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa kan fafaren hul a Lebanon.

"Za mu so mu ga an kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa fararen. Yana da matuƙar muhimmanci a ga cewa hare-haren ba su afka wa fararen hular da ba su ji ba su gani ba," kamar yadda mai magana da yawun Fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya gaya wa taron manema labarai.

Peskov ya yi kalaman ne a matsayin martani da tuhumar Isra'ila kan hare-haren sama aƙalla bakwai da ta kai kudancin wajen birnin Beirut a ranar Lahadi da yamma, a wani mummunan ba-ta-kashi da ba a yi irinsa ba tun ɓarkewar rikicin a bara, a cewar kafar yaɗa labaran ƙasar Lebanon.

Peskov ya ffayace muhimmanci tabbatar da cewa an ba da hanyoyi da dama na shigar da kayan agaji cikin yankunan da ake rikici a Gabas ta Tsakiya.

Kakakin ya kara da cewa, "Saboda rikicin jinƙai ba wai kawai yana kara karfi ba ne, idan muka yi magana game da Gaza, to dukkanmu muna shaida mummunan rikicin jinƙai da ke faruwa a can."

Ya ci gaba da bayyana halin da ake ciki na jinƙai a Lebanon a matsayin na gaggawa.

1149 GMT Isra'ila ta kai sabbin hare-hare uku a Lebanon a ranar Litinin

Jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hare-hare uku a kudancin Beirut da ke Lebanon a ranar Litinin, jim kaɗan bayan Isra’ilar ta bayar da umarni ga mazauna yankin su yi hijira.

Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ruwaito cewa an kai hare-haren ne a unguwar Haret Hreik da Bir al-Abed duka da ke kudancin Beirut.

Mai magana da yawun sojin Isra’ila Avichay Adraee ya wallafa taswirar gidajen da harin ya faɗa a kansu a shafinsa na X, inda ya yi iƙirarin cewa akwai kayayyakin Hezbollah a ciki.

0803 GMT Akwai yiwuwar sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon nan da kwana biyu, kamar yadda kafar watsa labaran Isra’ila ta ruwaito.

Kafar watsa labarai na KAN ya ruwaito wata majiya ta Isra’ila na cewa Benjamin Netanyahu ya amince da batun yarjejeniyar tsagaita wuta da Lebanon wadda Amurka ke goyon baya.

Kamar yadda kafar watsa labaran ta ruwaito, Netanyahu ya amince wa jakadan Amurka Amos Hochstein ya ci gaba da aiki kan batun yarjejeniyar da Lebanon.

Majiyar ta Isra’ila ta bayyana cewa tuni aka kammala cim ma yarjejeniyar inda a halin yanzu Netanyahu ke aiki kan yadda zai fitar da sanarwar.

2151 GMT — Wakilin Amurka Amos Hochstein ya yi barazanar janyewa daga sanya baki wajen ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon idan mahukuntan Tel Aviv ba su amince da shawarar Amurka ba, kamar yadda gidan talbijin na Isra'ila Channel 13 ya ruwaito.

Hochstein ya shaida wa jakadan Isra'ila a Amurka, Michael Herzog, cewa idan shugabanni a Tel Aviv suka ƙi yarda da shawarwarin Amurka kan yadda za a tsagaita wuta a Lebanon, Amurka za ta janye hannunta daga shiga tsakanin da take yi wajen ganin ɓangarorin biyu sun yi sulhu, a cewar tashar ta talbijin.

Ƙarin labarai👇

0009 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye

Sojojin Isra'ila sun kashe wani yaro Bafalasɗine tare da wani matashi a harin da suka kai a garin Ya'bad da ke kudancin birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar da wannan labari a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce Isra'ila ta kashe Muhammad Hamarsheh, ɗan shekara 13 da Ahmad Zaid, ɗan shekara 20.

Kamfanin dillanacin labaran Falasɗinu,WAFA, ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sn kutsa cikin garin Ya'bad ta gabashin garin, lamarin da ya haddasa taho-mu-gama tsakaninsu da mazauna yankin.

TRT Afrika da abokan hulda