Magoya bayan tsohon Firaiministan Pakistan Imran Khan wanda ya kafa jam'iyyar Tehreek-e-Insaf kenan gabanin zanga-zanga a Islambad don neman a sake shi daga gidan yari.              

Dubban magoya bayan tsohon firaministan Pakistan Imran Khan wanda ke ɗaure a gidan yari ne suka gudanar da zanga-zanga a Islamabad a daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ta kama mutum sama da 4,000 tare ɗaukar tsauraran matakan tsaro don daƙile zanga-zangar.

Masu zanga-zangar dai, sun amsa kiran Khan na a gudanar da ''tattakin ƙarshe,'' suna masu neman a sake shi daga gidan yari da kuma neman murabus ɗin gwamnatin Firaiministan Shehbaz Sharif.

Tashe-tashen hankulan dai sun janyo tsaiko a wasu sassan ƙasar, lamarin da ke kara nuna tabarbarewar harkokin siyasa a Pakistan, a yayin da ƙasar ke fama da ƙalubalen tattalin arziki.

Tsare dubban mutane

Gwamnatin Pakistan ta ɗauki tsauraran matakai don dakile zanga-zangar, tare da tsare dubban magoya bayan jam'iyyar Khan ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) tun ranar Juma'ar da ta gabata.

An dakatar da zirga-zirgar ababen hawa, sannan an rufe manyan tituna da ke zuwa babban birnin ƙasar. An kuma katse hanyoyin sadarwa ta waya da kuma intanet a muhimman warare, kazalika an hana taron mutane sama da mutum hudu a Islamabad.

Duk da waɗannan matakan, magoya bayan PTI - ƙarkashin jagorancin fitattun mutane a jam'iyyar kamar matar Khan, Bushra Bibi da kuma babban ministan yankin Khyber Pakhtunkhwa Ali Amin Gandapur - suna ci gaba da matsa lamba tare da cire shingayen da aka sanya a kan hanyoyi da kuma yin arangama da jami'an tsaro.

Bidiyoyi da ke yawo a shafukan intanet sun nuna masu zanga-zangar suna amfani da manyan injuna wajen cire shingayen, inda wasu kuma suka yi arangama da 'yan sanda.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun ƙona itatuwa, yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsashin roba wajen tarwatsa jama’a.

Matar Khan ta yi jawabi ga magoya bayan daga cikin wata babbar mota, inda ta buƙace su da yin tsayin daka don ''cim ma muradunsu'' da kuma neman a 'yantar da Khan.

Jam'iyyar PTI ta ce zanga-zangar ta janyo dubban mutane daga sassan ƙasar, ko da yake jami'an gwamnati sun ƙiyasta adadin ya kai kusan mutum 10,000.

Martani mai tsauri

Gwamnati ta sanya dokar hana fita ta kwanaki biyu a Islamabad da kuma yankunan da ke makwabtaka da ita, inda aka tura dubban 'yan sanda da jami'an tsaro da kayan aiki.

An toshe manyan tituna ciki har da Titin Grand Trunk, sannan an dakatar da zirga-zirgar jama'a a lardin Punjab don hana masu zanga-zangar isa babban birnin ƙasar.

Ministan Harkokin Cikin Gida Mohsin Naqvi ya yi gargadin cewa, duk wanda ya karya dokar hana taruka zai fusknaci hukuncin kame. Sama da magoya bayan PTI 4,000 ne rahotanni suka ce an tsare su tun daga ranar Juma'a da ta wuce.

Kazalika an tsaurara matakan tsaro saboda ziyarar da shugaban ƙasar Belarus, Alexander Lukashenko ya shirya kaiwa birnin Islambad a ranar Litinin.

Zanga-zangar ta faɗaɗa

Zanga-zangar ta janyo hankulan ƙasashen duniya, inda magoya bayan jam'iyyar PTI suka shirya gangami a ƙasashe sama da goma sha biyu a faɗin duniya.

Bidiyoyin da aka yi ta yadawa a intanet sun nuna yadda aka gudanar da manyan taruka a Birtaniya da Italiya da Amurka da kuma Australia, inda mahalarta taron ke neman a saki Khan tare da zargin gwamnatin Pakistan da hana harkokin siyasa gudana.

PTI ta ce 'yan Pakistan a ƙasashen waje na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa buƙatarta na neman a gudanar da bincike kan zargin maguɗin zaɓe da aka yi a babban zaben ƙasar da aka gudanar a ranar 8 ga watan Fabrairu na 2024 da kuma sakin fursunoni 'yan siyasa da aka kama.

Jam'iyyar ta kuma yi kira kan a sake fasalin fannin shari'a ƙasar don inganta harkokin siyasa

Babban al'amari

Imran Khan, wanda ya taba zama fitaccen ɗan wasan kurket a duniya, ya kasance jigo a siyasar Pakistan. Ya kuma riƙe muƙamin firaministan Pakistan daga watan Yulin 2018 zuwa Afrilun 2022 bayan nan aka cire shi da muƙamin.

Tun bayan da aka ɗaure shi a watan Agustan 2023, Khan ya fuskanci tuhume-tuhume da dama kan cin hanci da rashawa da dai sauransu, ko da yake an yi watsi da wasu daga cikinsu bayan ɗaukaka kara.

Duk da hakan, yana ci gaba da zama a gidan yari saboda shara'ar da ake ci gaba da gudanarwa a kansa. Gwamnati ta musanta ikirarin jam'iyyar PTI na nuna son kai a shari'a, tana mai cewa ana gudanar da shari'ar Khan ba tare da nuna son kai ba.

Gwamnatin firaiminista Shehbaz Sharif ta soki zanga-zangar, inda ta zargi PTI da janyo rashin zaman lafiya a ƙasar a lokacin da take gudanar da muhimman harkokin diflomasiyya.

TRT World