Ellie T. (ba sunanta ne na gaskiya ba), ‘yar shekara 29 wadda ta tsira daga cin zarafin ta hanyar lalata, tare da jaririnta ɗan watanni 3 a Port-au-Prince, Haiti, Yuli 23, 2024. / Hoto: Nathalye Cotrino/Human Rights Watch  

Duk da rikice-rikice tsakanin ƙungiyoyi ta'addanci a Haiti sun ragu a shekarar 2024, ana daɗa samun hare-hare kan fararen-hula, ciki har da ƙaruwar ''mummunan cin zarafi ta hanyar lalata," a cewar wani sabon rahoton ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch (HRW).

"A mafi yawan lokuta, ƙungiyoyi masu aikata laifuka sukan yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen tsorata mutanen yankunan da suke faɗa da su, kamar cin zarafi ta hanyar lalata," a cewar ƙungiyar.

''Ƙungiyoyin 'yan ta'adda ba sa mutunta doka a Haiti, idan aka yi la'akari da yadda suke yi wa 'yan mata da mata fyaɗe ba tare da wata fargaba kan ko wane irin hukunci ba,'' a cewar wani mai bincike da wata jami'a ta ƙungiyar HRW Nathalye Cotrino ta fitar.

HRW ta ce ta gudanar da bincike ta hanyar hirarraki da mutane da dama waɗanda suka tsira daga cin zarafi ta hanyar lalata da su da kuma jami'ai da sauran ma'aikatan jinƙai da na kare hakkin 'yan'adam a ƙasar da ke fama da talauci a yankin Caribbean.

Ƙungiyar ta ce daga watan Janairu zuwa Oktoba na wannan shekara, ''kusan 'yan mata da mata 4,000 ne aka samu rahoton an ci zarafin su ta hanyar lalata, ciki har da fyaɗe daga gungun mutane.''

Kazalika, ƙungiyar ta ba da misali da wani binciken Majalisar Ɗinkin Duniya na samun kaso 1000 a rahoton yaran da aka ci zarafinsu daga shekarar 2023.

''Yan ta'addan ba su damu da shekarun su ba,'' a cewar wani ma'aikacin agaji. '' Suna yin fyaɗe ne saboda suna da iko a hannunsu. Wasu lokuta sukan shafe kwanaki ko makonni suna aikatawa,'' inda sukan bar matan da suka tsira ɗauke da juna biyu - a ƙasar wadda ta hana zubar da ciki - ko kuma su ji musu rauni ba tare da sun samu wata kulawa ba.

Wata uwa mai shekara 25 ta ce wani gungun maza ne ya yi mata fyaɗe, a yayin da ta je nema wa 'ya'yanta ruwa.

''A baya dai, ba su yin haka, amma yanzu suna aikata duk abin da suke so," in ji ta.

Laifin fyaɗe ya zama ''ruwan dare, ta yadda yawancin matan da suke zuwa wurinmu suna cewa, 'Sun yi min fyaɗe, amma na yi sa'a ba su kashe ni ba," kamar yadda wata ma'aikaciyar agaji ta bayyana.

Rikicin da ke ci gaba da ta'azzara a Haiti dai, na gab da ruguza tsarin kiwon lafiyar ƙasar baki ɗaya.

Ƙungiyar Doctors Without Borders, wacce aka fi sani da MSF a harshen Faransanci kana wacce ta daɗe tana samar da kulawar gaggawa kyauta a babban birnin Haiti Port-au-Prince, ta dakatar da ayyukanta a birnin bayan hare-haren da aka kai wa ma’aikatanta da kuma “barazanar kisa da fyaɗe ga ma’aikatan MSF daga mambobin ƙungiyar 'Yan sandan ƙasar Haiti."

Hare-haren baya bayan nan da aka fuskanta sun biyo bayan zargin cewa MSF na ba da tallafin magunguna ga ƙungiyoyin ta'addanci a ƙasar.

Sai dai ƙungiyar ta musanta zargin tana mai cewa "tana ba da tallafi ne ga duk wanda ke buƙatar kulawar lafiya."

TRT World
AFP