Amurka na amfani da Taiwan domin jawo babban rikici a nahiyar Asiya, kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Andrei Rudenko ya shaida wa kamfanin dillancin labaran TASS a wani jawabi da aka wallafa a ranar Lahadi, inda yake ƙara jaddada goyon bayan Moscow ga China dangane da rashin jituwarta da Taiwan.
"Mun ga cewa Washington, ta saba wa ka'idar "China daya" da ta amince da ita, tana karfafa huldar soja da siyasa da Taipei a inda take fakewa da batun 'kowa ya tsayawa inda yake', da kuma kara samar da makamai," kamar yadda Rudenko ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar.
“Burin irin wannan katsalandan ɗin na Amurka a yankin shi ne harzuƙa jama’ar China da kuma jawo rikici da zai biya buƙatun Amurka.
China na kallon Taiwan a matsayin yankinta, lamarin da gwamnatin Taiwan ta ki amincewa da shi.
Amurka ce ƙasar da ta fi goya wa Taiwan baya da kuma samar mata da makamai duk kuwa da rashin amincewa da Taiwan ɗin a hukumance.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba ta mayar da martani nan take ba game da zargin da Rudenko ya yi ba.
A watan Satumba, Shugaba Joe Biden na Amurka ya amince da dala miliyan 567 domin tallafa wa ɓangaren soji na Taiwan.
Sai dai Rasha ta mayar da martani inda ta ce tana tare da China dangane da batutuwan da suka shafi yankin na Asiya, inda kuma ta caccaki Amurka kan shirin da take na jawo rikici a nahiyar.
China da Rasha a watan Fabrairun 2022 sun ƙaddamar da wani ƙawance “maras iyaka” a tsakaninsu a lokacin da Shugaba Vladimir Putin ya kai ziyara Beijing jim kaɗan kafin ƙaddamar da cikakken yaƙi kan Ukraine.