0351 GMT — Dakarun Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a sassa daban daban na Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 19 tare da jikkata wasu da dama.
A cikin wata sanarwa da hukumar kiyaye farar hula ta Civil Defence ta fitar ta ce, an kai hare-hare ta sama a unguwar Sabra da ke kudancin birnin Gaza, inda aka auna gidajen iyalan Abu Shanab, Kiyyali da Al-Lawh, inda suka kashe mutum tara tare da jikkata wasu da dama.
Majiyoyin lafiya sun ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan babura biyu a kudancin Gaza, inda suka kashe mutane uku.
Wani hari na daban da aka kai ta sama a tsakiyar birnin Gaza da kuma kudancin birnin Rafah ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Falasdinawa shida tare da jikkata da dama.
Kazalika, wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu a cewar rahotannin cikin gida.
0351 GMT — Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 10 a wani hari da ta kai kan sansanin al-Shati da ke Gaza
Akalla Falasdinawa 10 ne suka mutu, uku kuma suka jikkata, a wani harin da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Shati da ke yammacin birnin Gaza, in ji majiyoyin lafiya.
Sojojin Isra'ila sun kai hari kan Falasdinawa da ke kan layin neman ruwa a sansanin, in ji majiyoyin.