Yadda harin bam ɗin Isra'ila ya kashe Khaled Nabhan, kakan fitacciyar yarinyar 'soul of my soul' da Isra'ila ta kashe

Yadda harin bam ɗin Isra'ila ya kashe Khaled Nabhan, kakan fitacciyar yarinyar 'soul of my soul' da Isra'ila ta kashe

Dattijon ya ja hankalin duniya da kalamansa na bankwana mai sosa zuciya wanda ya yi wa jikarsa Reem bayan wani harin sama na Isra'ila ya kashe ta a Gaza a shekarar 2023.
Bayan ya rasa jikokinsa, Khaled Nabhan ya nuna bakin cikinsa ta hanyar da ta sosa zukatan al'ummar duniya. / Hoto: TRT World  

Khaled Nabhan, kakan wata yarinya Bafalasɗiniya da ya nuna alhininsa a yayin bankwana da jikarsa Reem wadda wani harin Isra'ila na sama ya kashe ta, inda ya kira ta da ''ruhin raina''

“Ruhin raina. Ita ce ruhin raina.”

Kalaman Khaled Nablan kenan a yayin da yake bankwana mai ratsa zuciya ga jikarsa Reem 'yar shekara 3 da haihuwa, wacce aka kashe tare da ɗan uwanta ɗan shekara 5, Tarek, a wani harin jiragen yakin Isra'ila kan sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a kudancin Gaza a ranar 22 ga watan Nuwamban 2023.

An ɗauki hotuna da bidiyo na yanayin mai sosa zuciya da duniya ta shaida mutumin da alhini da kuma ƙaunarsa ga jikarsa da suka nuna irin wahala da ƙuncin da Falasɗinawa suke fama da su.

A ranar 16 ga Disamban 2024, ruwan bama-baman Isra'ila suka afka kan sansanin da Khaled ya taɓa makokin jikokinsa. Mutuwarsa ta kawo ƙarshen rayuwar tashin hankali da ya shiga a bara, wacce ta sosa zukatan al'ummar duniya.

Yadda Khaled Nablan ya yi Bankwana da jikarsa

Duniya ta fara shaida Khaled ne ta hanyar hotuna da bidiyonsa rike da gawar jikarsa Reem, inda a hankali yake goge tarkacen kurar da ke fuskarta, yana shafa gashinta, yana kuma sumbatar gashinta. Muryarsa tana rawa yayin da yake kiran ta ''Ruhin raina.''

Yanayin ya kasance mai ratsa zuciya da ke nuna tsantsar bakin cikin rasa 'yar da ta kasance haske a cikin rayuwarsa.

''Lokacin da na furta waɗannan kalmomin, sun fito ne a daga zuciyata,'' kamar yadda Khalid ya shaidawa TRT a wata hira da aka yi da shi, yana mai ƙari da cewa, bai san ma ana daukar shi bidiyo ba sakamakon yanayin ƙunci da tashin hankali da yake ciki.

An yi ta yaɗa bidiyon Khaled da Reem wacce take wasa cikin farin ciki kafin rasuwarta, yanayin da ya taɓa miliyoyin mutane.

Mutane da dama sun yi ta yaɗa labarin a kafofin TikTok da Instagram da sauran shafukan sada zumunta ta hanyar tura sakonnin alhini da goyon bayansu.

Sai dai martanin Khaled kan mumunan bala'in da ya faɗa ciki bai tsaya kan iya makokin ba.

Gadon juriya

Shaidar da Nabhan ya bar wa duniyar nan ita ce juriyar Falasɗinawa.

A makonnin da suka biyo bayan mutuwar Reem da Tarek ne, Khaled ya mayar da bakin cikinsa zuwa aikace-aikace jinƙai.

A lokuta da dama, akan ganshi yana taimakon iyalan da suka jikkata a asibitocin da ke kusa da gidansa.

Ya kuma ƙaddamar da wani shirin jinƙai mai suna, Reem: Soul of the Soul, wanda ya sadaukar wajen faranta wa yaran Gaza ta hanyar rarraba musu kayan wasa da kyaututtuka.

A shafinsa na Instagram, wanda ya samu mabiya kusan miliyan ɗaya, Khaled ya wallafa wani shiri na musamman kan rayuwa a Gaza a yayin yakin da ke ci gaba da gudana. Saƙonnin da ya wallafa a shafin sun fallasa uƙuba da ɓarna da kuma tashin hankalin da ɗan'adam yake shiga a yanayi na yaƙe-yaƙe, inda suka nuna wa duniya yadda rayuwa take a cikin mamaya.

Duk da asarar da ya yi mai yawa, Khaled ya kasance, alama ta juriya. Bayan tsagaita buɗe wuta na ɗan wani lokaci a watan Nuwamban 2023, ya koma gidansa da aka lalata, yana mai tunawa da jikokinsa. Ya ɗauki rashinsu da ƙima tare da ƙudurin mayar da taƙaitacciyar rayuwarsu zawa mai ma'ana ta hanyar ayyukansa.

A yanzu, da aka kai kwanaki 437, yakin Isra'ila a Gaza ya kashe Falasdinawa sama da mutum dubu 44,976 tare da jikkata 106,759.

TRT World