Yawan wadanda suka mutu a yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya kai 45,129 / Hoto: Reuters

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri'ar neman Kotun Duniya ta ICJ ta bayyana ra'ayinta kan wajibcin da ke kan Isra'ila wajen ganin an isar da agajin da ƙasashe da ƙungiyoyin kasa da kasa ciki har da MDD ke bayar wa ga Falasdinawa

Majalisar mai wakilai 193 ta amince da ƙudurin da Norway ta tsara, inda ƙasashe 137 suka kaɗa ƙuri’ar amincewa. Isra'ila da Amurka da wasu kasashe 10 sun kaɗa kuri'ar rashin amince wa da shi, yayin da ƙasashe 22 suka ƙaurace.

Matakin dai ya zo ne a matsayin martani ga matakin da Isra'ila ta ɗauka na dakatar da ayyukan Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta MDD ga Falasdinu UNRWA a ƙasar daga ƙarshen watan Janairu, da sauran tarnaƙi da wasu hukumomin MDD suka fuskanta a ayyukan agajin da suke yi a Gaza cikin shekara guda.

Kotun ta ICJ, wacce aka fi sani da Kotun Duniya, ita ce kotun ƙoli ta Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma ra'ayoyinta na ba da shawara na da muhimmanci ta fuskar doka da siyasa ko da yake ba dole ne a yi aiki da su ba.

1244 GMT — Akalla karin Falasdinawa 32 aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 45,129, in ji ma’aikatar lafiya a yankin.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 107,338 kuma sun samu raunuka a harin da ake ci gaba da kai wa.

Ma'aikatar ta ce: Sojojin Isra'ila sun kashe mutane 32 tare da raunata wasu 94 a kisan gilla da aka yi wa iyalai hudu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

0837 GMT — Harin da Isra'ila ta kai cikin dare a Gaza ya kashe ƙarin Falasɗinawa

Kimanin Falasdinawa 20 da suka hada da yara da dama ne aka kashe a hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare a Gaza, in ji likitoci.

Kakakin hukumar kiyaye farar hula Mahmoud Basal ya ce an tsamo gawawwakin mutum 18 daga karkashin baraguzan gidaje uku bayan harin da Isra'ila ta kai a birnin Gaza da kuma arewacin yankin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce akwai yara bakwai daga cikin wadanda lamarin ya shafa.

A gefe guda kuma, an kashe miji da matarsa ​​a wani harin da Isra'ila ta kai gidansu da ke sansanin 'yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta bayyana.

0816 GMT — Dakarun Isra'ila sun tsare aƙalla Falasdinawa 14 daga yankuna daban-daban na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Daga cikin wadanda ake tsare da su har da wata mata 'yar Gaza da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan wadda ta je can domin neman magani, baya ga yara da wadanda ake tsare da su.

Baya ga haka Isra’ila ta sake kai hari kan wani gida da ke Jabalia a arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda sojojin na Isra’ila suka kashe aƙalla Falasɗinawa 10, kamar yadda majiyoyin kiwon lafiya suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters

TRT Afrika da abokan hulda