Alhamis, 23 ga Janairu, 2025
1214 GMT — Ma'aikatan kiwon lafiya na Falasɗinu sun gano sabbin gawawwaki 120 a ƙarƙashin ɓuraguzan gine-ginen da Isra'ila ta ruguza a Gaza, lamarin da ya sa adadin mutanen da ta kashe a yaƙin kisan ƙare-dangin da take yi a yankin tun watan Oktoban 2023 ya kusa kaiwa 47,283.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince da ita, har yanzu ba a san takamaimai adadin mutanen da Isra'ila ta kashe ba. A yayin da ake ci gaba da tono gawawwaki, ana sa rai adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru sosai.
Wata sanarwa da ma'aikatar kiwon lafiya ta fitar ta ce an kai mutum 306 da suka jikkata asibiti a awa 24 da suka gabata, lamarin da ya sa adadin waɗanda suka jikkata tun da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙin ya kai 111,472.
0600 GMT — Dakarun Isra'ila sun kai samame Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a yayin da suka mamaye Jenin
Dakarun Isra'ila sun kai samame a sassa daban-daban na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar wasu majiyoyi, a yayin da suka mamaye birnin Jenin.
Kamfanin dillacin labaran WAFA na Falasɗinu ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun kutsa cikin garin Turmusayya da ke arewacin Ramallah, kuma sun mamaye wasu muhimman gine-ginen gwamnati.
A Jenin, dakarun Isra'ila sun shiga ƙauyen Fahma inda suka riƙa harba tiyagas kan mutane, lamarin da ya kai ga arangama a tsakaninsu.
A Bethlehem, dakarun Isra'ila sun kai samame a garin al-Khader, inda suka mamaye Hanyar Birnin Ƙudus zuwa Hebron sannan suka riƙa fesa barkonon-tsohuwa kan 'yan kasuwa a cikin shagunansu, ko da yake ba a samu rahoton jikkata ba.
2100 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi magana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu domin jaddada goyon bayan Washington a gare su, sannan mutanen biyu sun tattauna game da Iran da kuma Isra'ila da ake garkuwa da su a Gaza, a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Wannan shi ne karon farko da Rubio ya yi magana da jami'an Isra'ila tun bayan da aka rantsar da Donald Trump ranar Litinin.
Trump da mutumin da ya gabace shi, tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, sun bayyana goyon yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza.
Rubio ya bayyana muhimmancin matakin " Amurka na ci gaba da goyon bayan Isra'ila a matsayin babban abin da Trump ya sanya a gaba," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar.
Rubio ya shaida wa Netanyahu cewa Washington za ta ci gaba da goyon bayan Isra'ila "ba tare da gajiyawa ba" domin ganin an ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
"Kazalika Sakataren Harkokin Wajen ya miƙa fatansa na ganin an daƙile duk wata barazana da ke fitowa daga Iran da kuma tabbatar da zaman lafiya," a cewar sanarwar.
2000 GMT — Dakarun Isra'ila sun sace ƙarin Falasɗinawa bakwai
Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙalla bakwai daga biranen Jenin da Jericho na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin WAFA ya ambato wasu majiyoyi suna tabbatawa.
"Dakarun mamaya sun yi wa Falasɗinawa huu ƙawanya; mata biyu iyayen wasu Falasɗinawa biyu da dakarun Isra'ila suka kashe a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin ," in ji kamfanin dillancin labaran na Falasɗinu.
Dakarun Isra'ila sun kai samame a birnin Jericho, lamarin da ya kai ga arangama, a cewar WAFA, inda kamfanin labaran ya ƙara da cewa dakarun an Isra'ila sun sace matasa biyu a yankin Silwan na Birnin Ƙudus.