gaza / Photo: AFP

Laraba, 22 ga Janairu, 2025

1428 GMT — Likitocin Falasdinawa sun gano gawawwakin Falasdinawa 53 daga karkashin baraguzan gine-gine a Gaza, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a yankin tun daga watan Oktoban 2023 zuwa 47,161, in ji ma'aikatar lafiya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, an kuma kwantar da mutane 19 da suka jikkata a asibitoci cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 111,166 a harin da Isra'ila ta kai.

"Mutane da yawa har yanzu suna makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto ba su iya isa gare su," in ji ta.

0830 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasɗine magidanci a gaban matarsa da 'ya'yansa uku yayin da yake tuƙa mota a birnin Jenin citda ke arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kutsawa yankin.

Wani bidiyo da iyalan mutumin suka ɗauka wanda aka riƙa watsawa a shafukan intanet ya nuna mawuyacin halin da Ahmed Nimer Obeidi Shayeb lokacin da aka harbe shi.

A yayin da yake tattaunawa da Anadolu Agency, Bashir Matahen, Daraktan Watsa Labarai na Birnin Jenin, ya ce Ahmed Shayeb yana tare da iyalansa - matarsa da 'ya'ya uku - suna hanyar komawa gida yayin da wani sojan Isra'ila gwanin harbi daga ɓoye ya buɗe masa wuta.

A gefe guda, Matahen ya ce Falasɗinawa fiye da 600 sun tsere daga sansanin 'yan gudun hijira na Jenin a yayin da dakarun Isra'ila suke ci gaba da kutsawa birnin na Jenin.

2224 GMT –– Isra'ila ta kai hare-hare a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kwanaki bayan bayan yarjejeniyar tsagaita a Gaza

Isra'ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare a birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla tara da jikkata aƙalla mutum 40, in ji jami'in kiwon lafiyar Falasɗinu, a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta ƙulla da Hamas ta shiga kwana na huɗu a Gaza.

A Tel Aviv, an jikkata mutum huɗu a wani hari da aka kai musu da wuƙa ko da yake jami'an tsaro sun kashe mutumin da ya kai harin, a cewar 'yan sandan Isra'ila.

Hukumomi sun ce mutumin da ya kai harin "ɗan ƙasar waje" kuma yana da shekaru 28 suna masu cewa harin na ta'addanci ne.

Mutanen Gaɓar Yammacin Kogin Jordan na ci gaba da fuskantar tsangwama daga Isra'ila./Hoto: AA

2100 GMT — Motocin agaji aƙalla 2,400 sun shiga Gaza

Kimanin motocin agaji 900 sun shiga Gaza a yayin da wani babban jami'i na MDD ya ce kawo yanzu babu wani ƙalubale da ya shafi karya doka.

Hakan na nufin a jumlace motocin agaji 2,400 sun shiga yankin wanda aka mamaye.

A watanni 15 da Isra'ila ta kwashe tana yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza, MDD ta bayyana shigar da kayan agaji yankin a matsayin babban ƙaluale — inda dakarun Isra'ila suke hana ma'aikatanta gudanar da ayyukansu sannan gungun 'yan Isra'ila suna sace kayan na agaji.

Muhannad Hadi, wani babban jami'i na MDD a Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ya ce a kwana uku da suka wuce ba a samu satar kayan agaji da yawa ba, "ba kamar a baya ba."

Falasɗinawa da dama a birnin Rafah na kudancin Gaza sun koma gidajensu sai dai sun yi matuƙar kaɗuwa da ganin yadda aka wawashe komai a shaguna da gidajen nasu. . / Photo: AFP

2000 GMT — An gano gawawwaki da suka zagwanye a ƙarƙarshin ɓuraguzan gidaje

Falasɗinawa da dama a birnin Rafah na kudancin Gaza sun koma gidajensu sai dai sun yi matuƙar kaɗuwa da ganin yadda aka wawashe komai a shaguna da gidajen nasu.

Manal Selim, wata mata mai 'ya'ya shida, da ke sana'ar gyaran gashi kuma tana da kantin sayar da kayan aure na mata, ta ce an sace komai daga shaguna da gidanta.

"Mun yi tsammanin za mu samu wani abu, ko kuma mu samu wurin zama," in ji ta. . "Ɓarnar ta girgiza mu."

A nasa ɓangaren, wani ma'aikacin agaji ya ce sun gano gawawaki da dama a ƙarƙashin ɓuraguzan gine-gine da Isra'ila ta ruguza.

"A cikin kwana biyu mun gano gawwaki 120 da suka zagwanye. Sun yi matuƙar zagwanyewa ta yadda ƙasusuwa ne kawai suka rage," a cewar Haitham Hams a hira da kamfanin dillancin labaran Associated Press.

TRT World