Jawabin farko na wa’adin Shugaba Donald Trump na biyu ya ƙunshi batutuwa kamar jawabin wa’adinsa na farko: gama-garin suka ga ƙasar da ya karɓi ragamar mulkinta da kuma manyan alƙawurra na magance matsalolin.
Shekaru takwas da suka wuce, Trump ya bayyana abin da ya kira "lalata Amurka " kuma ya yi alƙawarin kawo ƙarshensa nan-take. A ranar Litinin, ya bayyana cewa “faɗuwar” ƙasar za ta zo ƙarshe nan-take, lamarin da zai kawo "lokacin da Amurka za ta fi kyau a tarihi."
Ga wasu batutuwa daga cikin jawabin nasa:
Matsalolin duniya
"Wata guguwar canji tana kaɗawa faɗin ƙasar. Haske na bazawa kan duniya gaba ɗaya, kuma Amurka za ta iya amfani da wannan damar fiye da yadda ta taɓa yi, amma daga farko dole mu kasance masu gaskiya game da ƙalubalen da muke fuskanta."
Suka kan Biden
"A yanzu muna da wata gwamnatin da ba za ta iya warware ko ƙaramar matsala a cikin gida ba, yayin da kuma take ci gaba da shiga bala’o’i a ƙetare. Ta kasa kare ‘yan ƙasarmu masu bin doka da oda amma tana ba da mafaka da kariya ga masu laifi masu haɗari, waɗanda yawancin su daga kurkuku ko kuma asibitin taɓin hankali suke kuma suka shigo ƙasarmu ba bisa ƙa’aida ba daga ƙasashen duniya."
Shiga ƙasar
"Zan ayyana dokar ta-ɓaci a bakin iyakar ƙasarmu na kudu. Nan take za’a dakatar da shiga ƙasar ta hanyar da ta saɓa wa doka, kuma za mu fara tsara yadda za mu mayar da miliyoyin baƙi masu laifi zuwa inda suka fito."
"Za mu sake samun ‘yancin kanmu. Za mu sake tabbatar da tsaronmu. Za a sake daidaitar da ma’aunin adalci... za a sake mayar wa mutane imaninsu da arziƙinsu da dimokraɗiyyarsu da kuma ‘yancinsu... Daga yanzu faɗuwar Amurka ta ƙare."
Zuwa duniyar Mars
"Za mu bi bayyanannen haƙƙinmu zuwa cikin taurari, inda za mu harba ‘yan sama-jannatin Amurka domin dasa tutar Amurka kan duniyar Mars."
Yaƙe-yaƙen duniyar
"Muna da wata gwamnatin da ta ba da kasafin kuɗi mara iyaka wajen kare kan iyakokin ƙasashen ƙetare, amma ta ƙi kare kan iyakokin Amurka, ko kuma, mafi muhimmanci, kare mutanenta."
Jinsi biyu kawai
"Zan kuma kawo ƙarshen tsarin gwamnati na ƙoƙarin shigar da launin fata da jinsi cikin duk wani fannin rayuwa, na gwamnati ne ko na mai zaman kansa... Daga yau, zai kasance a tsarin gwamnatin Amurka jinsi biyu ne kawai ake da shi, namiji da mace."
"Muna da wani tsarin lafiya wanda ba ya iya biyan buƙata a lokacin bala’i, duk da haka ana ƙara kashe kuɗi a kansa fiye da ko ina a duniya. Kuma muna da wani tsarin ilimi da ke koya wa yaranmu su ji kunyar kawunansu, a yawan lokuta, su tsani ƙasarmu, duk da soyayyyar da muke matsananin nuna musu. Duk waɗannan za su sauya daga yau, kuma za su sauya cikin sauri."
Tsarewar Allah
"Cikin shekaru takwas da suka gabata, an wahalar da ni tare da ƙalubalance ni fiye da ko wane shugaban ƙasa a tarihinmu na shekara 250... Waɗanda suka nemi su katse tafiyarmu sun yi ƙoƙarin ɗauke ‘yancina kuma ɗauke rayuwata. Kuma cikin ‘yan watannin da suka wuce, a cikin wani fili mai kyau a Pennsylvania, harshashin mai kisa ya bi ta kunne na, nan-take na ji kuma na yi imanin, kuma har yanzu, cewa an ceci rayuwata ne domin wani dalili. Allah ya cece ni ne domin in sake mayar da Amurka ƙasa mai girma"
Haƙo dai, haƙo dai
"Yawan kashe kuɗin gwamnati da ƙarin kuɗin makamashi ne suka janyo matsalar hauhawar farashi. Kuma shi ya sa a yau zan ayyana dokar ta-ɓaci kan makamashi . Za yi ta haƙo mai da iskar gas."
Yaƙe-yaƙen haraji
"Nan-take zan fara sauya fasalin tsarin kasuwancinmu domin kare ma’aikata da kuma iyalan Amurka. Maimakon ƙaƙaba wa ‘yan ƙasarmu haraji domin azurta wasu ƙasashe, zamu sanya haraji kan ƙasashen ƙetare domin azurta ‘yan ƙasarmu."
Mashigin Panama
Amurka za ta “sake karɓe iko da” Mashigin Panama.
"Ba mu bai wa China ba, mun bai wa Panama ne. Kuma za mu sake karɓe iko da shi."