Talata, 21 ga Janairu, 2025
1616 GMT — Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da yake magana a kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, ya ce hotunan musayar fursunoni na nuna wanda ke girmama mutuncin dan'adam da kuma wanda ya yi watsi da shi.
"Turkiyya za ta ƙara ƙaimi wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin, tare da daukar tsagaita wuta a matsayin wata dama" a Gaza," in ji Erdogan a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin bayan taron majalisar ministocin kasar a Ankara.
Tun da farko, kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce yanayin lafiyar fursunonin Falasdinu da aka sako ya nuna "barna da mugunta" na Isra'ila.
"Hotunan matan uku da aka yi garkuwa da su sun nuna cewa suna cikin cikakkiyar lafiyar jiki da ta kwakwalwa, sabanin fursunoninmu wadanda bayyanarsu ta nuna rashin kulawa da gajiyawa," in ji Hamas a cikin wata sanarwa.
Ya kara da cewa "Wannan a sarari ya nuna babban bambanci tsakanin dabi'u da ka'idojin tsayin daka da kuma barna da azabtarwa na mamaya," in ji ƙungiyar.
1113 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 6 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare a birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda suka kashe Falasɗina aƙalla shida da jikkata mutum 35, a cewar jami'an Ma'aikatar Kiwon Lafiya.
Tun da farko Hukumar Falasɗinawa ta ce matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na janye takunkuman da aka sanya wa 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan ne ya tunzura su domin ci gaba da musguna wa Falasɗinawa.
"Janye takunkuman da aka sanya wa 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi zai ƙarfafa musu gwiwa wajen aikata ƙarin laifuka kan mutanenmu", a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinawa ta fitar.
0913 GMT —Trump ne tunzura Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna - Hukumar Falasɗinawa
Hukumar Falasɗinawa ta ce matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na janye takunkuman da aka sanya wa Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan shi ne yake tunzura su wajen cin zarafin Falasɗinawa.
"Cire takunkuman da aka sanya wa 'yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi zai ƙarfafa musu gwiwa wajen aikata ƙarin laifuka kan mutanenmu", a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinawa ta fitar.
Ma'aikatar ta jawo hankali game da hari na baya bayan nan da 'yan kama-wuri-zauna suka kai wa Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan wanda ya jikkaya mutum 21.
0706 GMT — 'Yan kama-wuri-zauna na Isra'ila sun kai hari a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, sun jikkata Falasɗinawa 21
Falasɗinawa fiye da 21 sun jikkata yayin da Isra'ilawa 'yan kama-wuri-zauna suka kai hari a garuruwa biyu na Falasɗinawa kusa da birnin Qalqilya a arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Ƙungiyar bayar da agaji ta Palestinian Red Crescent Society ta ce tawagarta ta likitoci ta bayar da magunguna ga mutanen da suka jikkata sakamakon harin na 'yan kama-wuri-zauna a garuruwan Jinsafut da Al-Funduq.
Mutanen sun kukkuje sakamakon dukan da 'yan kama-wuri-zauna suka yi musu, sannan dakarun Isra'ila suka fesa musu tiyagas, a cewar ƙungiyar bayar da agajin.
'Yan kama-wuri-zauna sun kai harin ne a yayin da ake ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wadda Qatar, Masar da Amurka suka shiga tsakani wajen ƙulla ta ranar Lahadin da ta gabata.
0112 GMT —Trump ya nuna shakku kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shakkunsa game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a yayin da aka tambaye shi kan ko yana da ƙwarin gwiwa game da yiwuwar aiwatar da dukka matakai uku na yarjejeniyar.
A yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishin shugaban ƙasa bayan sanya hannu kan dokokin shugaban ƙasa, Trump ya ce yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya ya yi kama da "wani babban wuri da aka rusa" kuma ya kamata a sake gina shi a wani tsari na daban.
Ƙarin labarai 👇
0107 GMT — Trump ya soke takunkuman da aka sanya wa 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Shugaban Amurka Donald Trump ya soke takunkuman da tsohuwar gwamnatin Biden ta ƙaƙaba wa Isra'ilawa 'yan kama-wuri-zauna bisa musguna wa Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda sabon shafin intanet na Fadar White House ya bayyana.
Shafin ya ce Trump ya soke Dokar Shugaban Ƙasa mai lamba 14115 wadda aka amince da ita ranar 1 ga watan Fabrairun 2024, wacce kuma ta amince a sanya takunkumai kan "mutanen da ke yin tarnaƙi game da zaman lafiya da tsaron Gaɓar Yammacin Kogin Jordan."