Tsare Yoon da aka yi, zai baiwa masu bincike damar ci gaba da yi masa tambayoyi, sannan akwai yiwuwar a tsawaita wa'adin wata shida idan aka same da shi da laifi / Hoto: AFP  

Shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige Yoon Suk Yeol ya kwana ɗaya a gidan yarin Seoul a matsayin wanda ke jiran shari'a bayan umarnin kotu na tsare shi har na tsawon kwanaki 20.

A makon jiya ne dai, Yoon ya kafa tahirin zama shugaban ƙasa mai ci na farko da aka taba tsarewa a Koriya ta Kudu.

Da farko dai an tsare shi ne na tsawon sa'o'i 48 don amsa tambayoyi don binciken ko yana da hannu wajen tayar da zaune tsaye da kuma yunkurin ayyana dokar soji a ƙasar a ranar 3 ga watan Disamba.

Ga wasu karin bayanai game da gidan yarin da ake tsare shi da kuma abubuwan da ake sa ran za su iya faruwa da tsohon mai gabatar da kara wanda ya zama shugaban kasa.

Daukar hoto da kuma kayan gidan yari

A yayin da ake tsare shi kafin a yi masa shari'a, an ɗauki shaida ta hotonsa kana an duba ''cikakkiyar lafiyarsa,'' a cewar wani jami'in gidan yarin.

''Ba wani abu bane idan kai shugaban kasa ne, ana daukar hoton kowa a lokacin da za a shiga da mutun cikin gidan yarin,'' in ji jami'in, wanda ya buƙaci a sakaye asalinsa saboda ba shi da izinin yin magana da kafofin yaɗa labarai a hukumance.

Binciken jikin mutum da ake yi ba kawai don a duba lafiyarsa ba ne har ma da ''ko yana ɓoye wani abu,'' in ji jami'in.

Shugaban Hukumar Gidajen Yarin Koriya ta Kudu Shin Yong- hae ya shaida wa kwamitin shari'a na majalisar dokokin ƙasar a ranar Litinin cewa, Yonn ya ''ba da haɗin-kai'' kuma an gudanar da aikin tsare ba tare da wata matsala ba.

Fursunonin da ake tsare da su kafin a yi musu shari'a irin Yoon, an ba su kayan gidan yari launin kunun kanwa, yayin da su kuma fursunonin da ake yanke musu hukunci suke sanye da kaya mai launin toka.

Yoon "ya kwana lafiya," in ji Shin.

Kurkukun mutum ɗaya

Bayan an kammala ɗaukar bayanansa, an tura Yoon zuwa sashen tsare fursunoni inda aka keɓe shi a kurkukun mutum ɗaya mai girman murabba'in mita 12 (taku 129), in ji Shin.

Wurin ya wuce murabba'in mita 3.4 da ake samu na kurkukun da ake ware mutum ɗaya.

Duk da sunan gidan yarin ''Seoul Detention Centre'' yana babban birnin Uiwang, mai tazarar kilomita 22 (mil 14) kudu da Seoul, a baya kuma ya yi suna wajen tsare manyan mutane ciki har da tsohuwar shugabar ƙasar Park Geun- hye da shugaban kamfanin nau'rorin Samsung Jay Y. Lee.

A matsayin wanda ke jiran a yi masa shari'a, Yoon zai tashi tare da sauran fursunoni da misalin karfe 6:30 na safe sannan zai kwanta da misalin karfe 9 na dare.

Sinadarin Calories 2,500

Hukumar da ke kula da gidajen yarin Koriya ta Kudu wadda ke sa ido kan sauran cibiyoyin tsare mutane a ƙasar, ta ce dokoki da kuma sashen bayananta sun tanadi abinci mai samar da kuzari da ke adadin Calories 2,500 a kowace rana ga fursunonin da ake tsare da su kan farashin kudin kasar Won 1,600 ($1.09).

Abinci wata al'ada ce a kasar, an ba wa Yoon nauyin abincin Kimchi da miyan wake da kuma gasashen nama a daren ranar Laraba da ya kwana ɗaya a tsare, a cewar bayanan gidan yarin.

Ba a samu cikakken bayanai ba game da nauyin karin kumallo da aka ba shi a ranar Litinin.

Kwanaki ashirin da wata shida

An kama Yoon ne a makon da ya gabata, a karkashin sammacin da ya ba hukumomi damar tsare shi na tsawon sa'o'i 48, wanda ake samu daga kotu idan wanda ake zargi da aikata laifi ya ki amsa sammaci ko ba da haɗin kai.

Dokar Koriya ta Kudu ta tanadi wani tsari da ya baiwa masu bincike damar tsare wanda ake zargi har na tsawon kwanaki 20, idan suka gano akwai wata matsala da za a samu a yayin bincike da suke gudanarwa.

Idan aka soma binciken, za a iya tsare wanda ake zargi har tsawon wata shida.

Hukumar binciken laifukan cin hanci da rashawa (CIO) da aka kafa a shekarar 2021 don binciken manyan jami'ai gwamnati da iyalansu ne ke jagorantar binciken da ake yi kan Yoon.

Ko da yake hukumar ba ta da hurumin gurfanar da shugaban kasa, kuma dole ne ta mika duk wata korafi ga ofishin masu gabatar da kara domin daukar mataki na gaba.

Reuters