1550 GMT — Jiragen saman Isra'ila sun kashe mutane tara a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat na Gaza
Falasdinawa 9 ne suka mutu yayin da wasu da suka hada da yara da mata suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.
Jiragen yakin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a gidaje da dama a garin Nuseirat, lamarin da ya yi sanadiyyar rugujewarsu gaba daya tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa Anadolu.
Majiyoyin lafiya a asibitin al-Awda sun shaida wa Anadolu cewa, tawagar ceto sun yi nasarar gano gawarwaki shida da suka hada da mata uku daga baraguzan gidajen da aka kai harin.
Sun yi nuni da cewa, har yanzu kungiyoyin agaji na ci gaba da kokarin gano wasu da dama da suka bata a karkashin baraguzan ginin.
1549 GMT — Italiya na fatan Iran za ta matsa lamba ga ƙawayenta don rage tashin hankalin yankin Gabas ta Tsakiya
Ministan Harkokin Wajen Italiya ya ce Rome na fatan Iran za ta yi tasiri sosai a kan ƙawayenta don kawar da tashin hankalin yankin Gabas.
Antonio Tajani "ya nanata tsananin damuwar gwamnatin Italiya, kuma a madadin kasashen G7, na tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza kamar yadda ake yi a Lebanon," a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar bayan ya gana da takwaransa na Iran Abbas Araghchi, a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York.
Tajani ya shaida wa Araghchi cewa Italiya tana fatan "Tehran za ta yi amfani da tasirinta a kan kungiyoyin da ke yankin, don kiran su zuwa tsaka-tsaki a kowane yanki: Lebanon, Iraki, Siriya da Bahar Maliya," kamar yadda ya jaddada ƙwarin gwiwar Rome na hana ci gaba da ta'azzara.
1548 GMT — Tilastawa Falasdinawan gudun hijira zai zama 'laifi na yaki': Sarkin Jordan a Majalisar Dinkin Duniya
Sarki Abdallah na biyu na kasar Jordan ya yi watsi da yiwuwar kasarsa ta zama wata ‘yar kasa ta musamman ga Falasdinawan, yana mai gargadin cewa korar da Isra’ila ke yi na tilastawa zama wani laifi ne na yaki.
"Ra'ayin mayar da Jordan a matsayin madadin mahaifar Falasdinawa... ba zai taba faruwa ba," kamar yadda ya shaida wa taron Majalisar Dinkin Duniya, ya kara da cewa Jordan "ba za ta taba amincewa da tilasta wa Falasdinawa gudun hijira ba, wanda hakan laifi ne na yaki."
0413 GMT –– Hezbollah ta harba makamai masu linzami kan sansanoni da kamfanin haɗa bam na Isra'ila
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta harba makamai masu linzami shida kan sansanonin soji da ke arewacin Isra’ila, daga ciki har da sansanin sojin sama biyu da wani kamfanin haɗa bama-bamai.
Hezbollah ɗin ta ce ta kai wannan harin ne domin mayar da martani kan irin yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta Lebanon ta fitar a Telegram, ta ce ta kai hari kan sansanin sojin sama na Megiddo da ke yammacin birnin Afula sau uku.
Wannan ne karo na farko da ƙungiyar ke kai hari kan sansanin sojin mai nisan kilomita 30 daga iyakar Lebanon.
A wata sanarwar ta daban, ƙungiyar ta tabbatar da cewa ta kai hari kan sansanin sojin sama na Ramat David da kuma Amos, waɗanda sansanoni ne masu muhimmanci na hada-hadar sufuri ga sojojin na Isra’ila.
Haka kuma Hezbollah ɗin ta kai hari wata masana'anta a garin Zichron Ya'acov da ke arewacin birnin Kaisariya, mai tazarar kilomita 60 (mil 37) daga kan iyakar kasar Lebanon, wadda ke samar da ababen fashewa.