Gidan rediyon Isra'ila ya ce yawan waɗanda suka jikkata kuma ya zarce 1,000. Hoto: AA

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce Falasdinawa 232 ne suka mutu sakamakon hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a Gaza bayan yi mata ƙawanya, a wani martani da ta mayar kan harin da ƙungiyar Hamas ta kai mata.

Ma'aikatar ta sanar a shafin sada zumunta cewa baya ga adadin waɗanda suka mutun da ke ƙaruwa, aƙalla Falasɗinawa 1,600 aka jikkata.

Kamfanin dillancin labaran Turkiyya, Anadolu ya rawaito kakafen yaɗa labaran Isra'ila na cewa aƙalla ƴan Isra'ila 300 harin na Hamas ya hallaka.

Gidan rediyon Isra'ila ya ce yawan waɗanda suka jikkata kuma ya zarce 1,000.

Har yanzu ana ci gaba da yakin da ake yi a kudancin Isra'ila," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar, tana mai cewa dakarun tsaro "na kare yankunan da Hamas ta kai hari."

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netayahu ya bukaci mutane su fice daga Gaza domin kuwa zai sa dakarun kasar su mayar da yankin da Hamas take fili fayau.

Asibitoci a fadin Isra’ila na faman kula da ɗaruruwan mutanen da suka ji rauni, inda a yanzu haka akwai mutum 460 da ake jinyarsu.

Cibiyar Lafiya ta Soroko a Beersheba ta ce tana kula da aƙalla marasa lafiya 280, inda 60 daga cikinsu ke cikin mummunan yanayi.

Rahotanni sun ce shi ma Asibitin Barzilai da ke Ashkelon a kusa da Gaza yana da majinyata 182 da aka ji wa rauni, kuma 12 daga cikinsu na cikin mummunan hali.

Ana tsammanin yawan waɗanda suka rasa rayukansu zai ƙaru.

AA